ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Ƴansanda Sun Saka Tukuicin Miliyan ₦50 Ga Wanda Ya Taimaka Aka Kama Wasu ‘Ƴan Bindiga 2

by Sani Abubakar
3 years ago
Miliyan

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina sun saka kyautar naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka ya bayar da bayanai da za su taimaka wajen kama ƙasurguman ƴan bindiga biyu da suka addabi wani yanki a jihar Katsina.

Ana zargin ƴan bindigar su ne, Modi Modi da takwaransa Jan Kare da kai muggan hare-hare a ƙananan hukumomin Safana da Ƙanƙara a baya-bayan nan.

  • Gwamnati Katsina Ta Kashe Miliyan 50 Wajen Gyara Motocin ‘Yansanda 15
  • ‘Yan bindiga Sun Kashe Mutum 6 A Jihar Katsina

Wannan dai na cikin wata sanarwa da kakakin ƴansandan Jihar Katsina Abubakar Sadiq ya fitar.

ADVERTISEMENT

Sadiq ya ce rundunar za ta tabbatar da ta ɓoye sunayen duk wanda ya taimaka ya ba da wani bayani da zai taimaka wajen kama waɗannan mutanen biyu.

Ya kara da cewa wannan na cikin matakan da ƴansanda da sauran takwarorinsu ke dauka wajen ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Sanarwar ta ce “Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta sanya naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka wajen bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama Modi Modi da Jan Kare da ke addabar yankin ƙananan hukumomin Safana da Ƙanƙara a jihar Katsina”.

Kakakin ƴansandan ya yi kira tare da ƙarfafa wa mutane guiwa da su fito su ba da bayanan da za su taimaka wajen kawar da ƴan bindigar.

Ya ce ga duk mai wani bayani da zai taimaka za su iya tuntuɓar waɗannan lambobin kamar haka: 07015142112, 08023871144.

Miliyan
Sani Abubakar
+ postsBio
  • Sani Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-abubakar-2/
    ‘Yan Ta’adda Sun Yi Yunƙurin Ƙwace Iko Da Sakatariyar Jihar Oyo
  • Sani Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-abubakar-2/
    Ƙarancin Ruwan Sha: Mai Mala Ya Ba Da Umarnin Kai Man Gas Wuraren Da Suke Da Rijiyar Burtsatsai
  • Sani Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-abubakar-2/
    Gwamnan Ondo Ya Sauke Kwamishinonin Jihar Baki Ɗaya
  • Sani Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-abubakar-2/
    Tsohuwar Ministar Jin Kai, Sadiya Ba Ta Ƙi Amsa Gayyatarmu Ba – EFCC

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Yadda Ake Kwakil Na Garin Filato Wanda Aka Fi Sani Da Waken Challa 

Yadda Ake Kwakil Na Garin Filato Wanda Aka Fi Sani Da Waken Challa 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.