Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai yi bayani ne a kan abubuwan da ke sa tumbi ha rya kai ga saw a mace muni a gidan miji. Da farko, idan kina son kauce wa tara irin wannan tumbin, ki tabbatar kafin ki kwanta bacci ka da ki ci abinci kowane iri, ana son a kalla ki samu kamar awa uku da gama cin abinci kafin kwanciya. Babu laifi ki dan samu wani abu mai dan dumi mara nauyi ki sha, yana taimakawa wajen narkewar abinci kafin kwanciya barci. A takaice yawan cin abinci latti ko kuma daga an gama a kwanta yana sa mace tumbi.
- Masu Son Fara Rubutu Su Zamo Masu Karatu Da Hakuri Koyaushe – Maryam Sakatariya
- Tsakanin Maza Da Mata, Wa Ya Fi Kazanta?
Akwai yanayin abinci da ruwan sha haka zalika akwai yanayin mu’amala ta yau da kullum dake sanya mata su zama masu tumbi, wannan zahiri ne domin binciken masana tumbi ya tabbatar da hakan.
Dangane da cin abu mai sanyi da safe bayan tashi daga bacci; ana so mace kafin ta ci komai ta sha abu mai dumi, ba a so a sha abu mai sanyi kamar lemo da yake da gas sosai a jikinsa, ki bari sai bayan kin sa abu mai dumi a ciki.
Yawan zama waje daya, ana so mace ta zama mai yawan motsa jiki musamman matan aure lokacin saduwa mace ta zama mai yawan motsa jikinta saboda yin hakan jikinta yana yawan mikewa ya yi daidai, amma mace ta kwanta kome miji ne zai yi yana sa jikin mace ya saki da wuri tumbi ya yi mata yawa.
Yawan cin abu mai maiko musamman mata masu zama waje daya yana kawo musa basir ya sa cikin mace ya kumbura ta zama mai tumbi kuma wanda ba shi da laushi ga yawan tusa.
Domin rabuwa da tumbi: Za ki samu lemon tsami ki yayyanka shi ki tace ruwan ki saka zuma kina sha sau biyu a rana safe da dare kafin kwanciya.
Za ki samu danyar kurkum wato tumerik da danyar citta sai ki fere su duka ki yayyanka su ki zuba a ruwa sannan ki yanka lemon tsami guda daya ki zuba sai ki samu kanunfari kadan da tafarnuwa ki zuba a ciki ki dafa, bayan ya dahu ki tace ruwan ki saka zuma kina sha.