Barkan mu da sake haduwa wannan makon Inda za mu duba yadda dan kasuwa zai tallata kaya a internet.
Internet wani tsari ne na hade_haden na’urorin duniya bisa bangare guda domin sadar da junansu a bisa dogon zango ba tare da hadakar waya a tsakani ba (wireless).
Idan ana so a fara sana’ar sayar da kaya ,a samu bangare daya ka mayar da hankalinka a kai misali, ko ka fara da bangaren jaka ko takalma ko kayan sakawa. ka mayar da hankalinka a kan abu daya domin fahimtar kwastomomin wannan bangaren. Misali, idan mu ka dauki bangaren sayar da jakunkuna matasa sun fi amfani da shi akwai masu son original, akwai masu son kwafi. ka zabi bangare daya ka fara yadda za ka fahimci kwastomomin wannan bangare yadda ya kamata.
Akwai kuma muhimmancin ganin cewa ba ka takaita kanka zuwa sayar da abu daya kawai ba, saboda idan abubuwa suka tafi yadda ake so, za ka fadada sana’ar domin sayar da wasu kayan daban. Idan har ka yi tunani haka, to ka yi tunani fadadawa zuwa kayan da suka dace da sana’ar ka ta farko. Misali idan ka na sayar da jaka ne za ka iya daga baya ka hada da kayan kwalliya.
Bayan ka yanke shawarar irin kayakin da kake so ka sayar, to ya kamata ka fara tara ma iya da kwastomomi a kan Intanet, shafin sada zumunta sune mafi saukin gudanar da haka idan ba ka da jari mai girma.
Kasuwancin ya fi kyau da tafiya a dandalin da za’a iya gina su, misali Instagram da facebook. matasa sun fi amfani da Instagram.
Bugu da kari, fahimtar irin abubuwan da mabiyanki da kwastomomin ki suka fi sha’awa na da muhimmancin sosai ga shafinki, saboda ba talla za ki riga sakawa ba, ki duba wace irin rayuwa suke tafiyarwa, menene yake burge su, wadanne irin matsalolin yau da kullum suke dama da su?
Duk za ki iya ba da ra’ayoyinki a nan, ke ma ki bayyana naki yadda hakan zai kara kulla dankon zumunta tsakaninku.
Tallan kaya ya fi tasiri idan aka nuna yadda mutane suke amfani da shi. Za ki iya daukar hotuna da kanki ko kuma za ki iya amfani da hotunan wanda ya sarar miki da kayan idan har suna da kyau kuma hotunan ainihi ne.
idan za ki iya samun wata wadda ta fiye wa al’umma ki bata jakar ta rike a yi hoto,to wannan zai taimaka kuma za’a yi sha’awar kayan. Allah ya taimaka.