Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake hada Fab Biskit:
Abubuwan bukata:
Fulawa 2 Kofi, Sukari–½ Kofi, Buta ½ Kofi, Kwai Daya, Bakin Fauda karamin cokali, Madara ta gari ko ta ruwa babban cokali 2, Filaibo (Banilla ko sururuberi ½ ), Gishiri kadan
- Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
- Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II
Yadda ake hadawa:
Ga yadda ake hada Fab biskit (wani irin biskit mai dandanon madara da sukari, mai taushi da dan kamshi kamar na “shortbread”).
Da farko za ki samu roba haka sai ki zuba sukari da Bota, ki cakuda su da cokali ko maburkaki har sai sun hade jikinsu kuma sun yi laushi. Sannan ki fasa kwai a ciki, ki zuba filaibo, ki ci gaba da cakudawa.
A wani kwano ko robar daban, ki hada fulawa, bakin fauda, madara, da dan gishiri. Sai ki zuba wannan hadin a cikin wancan kayan da kika fara hadawa. Ki gauraya su sosai har sai ya zama kullu mai laushi, ba mai taurin gaske ba.
Idan ya yi tauri, ki kara dan madarar ruwa ko dan mai ko buta. Ki baza kullun a faffadan tire, ki yi masa rolling ki yanka da cutter ko roba da siffar da kike so. Ki sanya a cikin tanderu mai dan zafi (180°C) na minti 15–20 har sai ya fara yin kalar kasa kasa).
Ki fitar ki barshi ya huce kafin ki adana.














