Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Ado Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake hada Mimi Fankek:
Abubuwan da za ku tanada:
Filawa, Suga, Baikin Fauda, Gishiri Bakin Soda, Mai, Kwai, Madara, Banilla Filaibo:
Yadda za ku hada:
Idan kuka samu filawa kamar kofi daya, sai suga kamar babban cokali biyu, sai gishiri kadan haka, sai baikin fauda rabin babban cokali , baikin soda rabin babban cokali, kwai daya, sai mai babban cokali biyu, madara rabin kofi.
Sai ki tankade filawar sannan ki zuba suga ki zuba gishiri baikin fauda ki zuba duk kayan da na ambata sai ki cakuda su gaba daya, ki dame su sosai, sannan ki dora firayin fan dinki idan ya danyi zafi sai ki fara zubawa daidai fadin da kike so, sannan za ki iya yi mishi dan kunne haka a sama zai dauki hankalin yara, amma za ki rage wuta ne sosai saboda shi baya son wuta, idan wuta ta yi masa yawa zai kone.
Yadda za ki gane kasan fankek din ya yi za ki ga ya dan bubbule a sama, wanda hakan alama ce ta kasan ya yi, sai ki juya shi saboda saman ma ya yi.
Za ki iya shan sa da shayi lokacin karin kumullo, ko kuma za ki iya sha da lemo da duk dai abin da kike so ko haka ma ana ci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp