Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda Za ku Hada Yagot A gida.
- Trump Ya Gayyaci Mark Zuckerberg Cin Abinci
- Cimma Burin Rage Salwantar Abinci A Kasar Sin Zai Samar Da Mafita Ga Duniya
Abubuwan da za ku tanada:
Madara ta gari, suga, Yagot ko nono kindirmo, filaibo,
Yadda za ku hada:
Da farko idan kuka samo madararku ta Gari kamar mudu daya haka sai ku zuba a tukunya, ku samu ruwa kamar lita biyu ku dama madarar ta damu sosai kada ta yi kulakulai za ku iya sa maburkaki wato bulugari wasu suke cewa, sai ku burkaka shi sannan sai ku kara ruwa kamar karamin kofi daya, saboda idan ya tattafasa ya zama wannan karamin kofi ya zama daidai lita biyu kenan.
Daga nan sai ki rufe ku dora a wuta, amma ku tsaya a wajen saboda kar ya yi funtu ya zuba, da zarar ya tafasa sai ki dan bude saboda kar ya rika zuba ku bar shi ya ci gaba da tafasa kamar tsawon minti 10 zuwa 15 haka ya dahu sai ku sauke shi ku ajiye shi a waje mai tsafta sannan ki bude shi ya sha iska.
Idan ya rage zafi ya zama akwai dumi wato shi bai huce ya zama san yi ba sannan kuma babu zafi sosai sai ki samu wani bokiti ku zuba a ciki sannan ku kawo Yagot ko kindirmo duk wanda kuka tanada ku zuba kamar lodayi daya sannan sai ku sa shi a waje mai dumi ku rufe ku bar shi ya yi kamar awa goma sha biyu, bayar wadannan awoyin da ya yi idan kuka dakko za ku ga ya zama Yagot, sannan ku zuba filebo ku burkaka shi, Sai ku sa shi a firij ya yi san yi, a sha dadi lafiya.