Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amsa gayyatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), dangane da zarginsa almundahana.Â
A cewar wata sanarwa daga ofishin yada labaran Yahaya Bello, ta ce ya yanke shawarar amsa gayyatar ne bayan tattaunawa da iyalansa, lauyoyinsa, da abokan siyasarsa.
- Karshen Bello Turji Ya Kusa Zuwa – Gwamnan ZamfaraÂ
- An Kammala Bikin Baje Kolin CIFTIS Tare Da Nasarori Masu Tarin Yawa
Daraktan yada labaran Bello, Mista Ohiare Michael, ya jaddada cewa Bello yana girmama doka kuma ya kasance yana wakiltar kotu ta hannun lauyoyinsa.
Yanzu ya yanke shawarar zuwa wajen EFCC domin ya wanke kansa, kasancewar ba shi da abin da zai boye.
Kazalika, tsohon gwamnan yana goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi.
Bello, tare da rukunin mutanen da suka raka shi, yana fatan EFCC za ta yi aiki da kwarewa kuma ta mutunta hakknsa a matsayinsa na dan kasa.
Za a bayyana cikakken bayani game da ganawarsa da hukumar nan gaba, kasancewar tsohon gwamnan yana fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da cin hanci kan wannan zargi.