A wani gagarumin mataki da kungiyar kwadago ta dauka na cimma bukatarsu ta neman mafi karin albashi, kungiyar ta rufe dukkan hanyoyin shiga na filin sufurin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas da kuma filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Matakin dai ya kawo cikas ga ayyukan jirgin, inda fasinjoji suka yi jungun-jungun a harabar filayen jirgin na kasa.
- Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ma’aikatun Gwamnati, Bankuna A Abuja
- Taron Karawa Juna Sani Kan Wayewar Kan Kasar Sin Ta Zamani Ya Bukaci Karin Nasarori A Fannin Ilimi
Rufe filayen ya biyo bayan umarnin da kungiyoyin ma’aikatan jiragen sama suka ba mambobinsu na janye ayyuka a dukkan filayen tashi da saukar jiragen sama a Nijeriya, bisa bin umarnin hadin gwiwa na NLC da TUC.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kungiyar kwadagon ta sanar da shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani a fadin kasar, sakamakon kin amincewa da gwamnatin tarayya ta yi na kara mafi karancin albashi daga N60,000.