Mambobin kungiyoyi daban-daban na kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC da TUC a safiyar ranar Litinin sun rufe ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ciki har da wasu ma’aikatun gwamnati da ke tsakiyar birnin tarayya Abuja domin tabbatar da bin umarnin kungiyar na tsunduma yajin aiki a fadin kasa baki daya.
Wakilin LEADERSHIP da ya ziyarci harabar ofishin shugaban ma’aikata da wasu ma’aikatu, ya ruwaito cewa da misalin karfe 9:00 na safe ‘yan kungiyar sun hana ma’aikata shiga ofishi.
- Gobe Za a Tsunduma Yajin Aiki, An Gaza Cimma matsaya Tsakanin Gwamnati Da NLC
- Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Rufe Kamfanin TCN Na Kasa
Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Kwamared Ahmed Sylvester Abba ya shaida wa LEADERSHIP cewa, ya yi murna da yadda ma’aikata ke goyon bayan yajin aikin da kungiyar ta tsunduma.
Shugaban kungiyar, ya jaddada cewa, dole ne gwamnatin tarayya ta biya ma’aikata albashin da ya dace da tsadar rayuwa.