Iyayen Dalibai a karkashin kungiyar malamai da iyaye ta kasa NAPTAN, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fara duba rahoton kwamitin Farfesa Nimi Briggs wanda ya gana da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, kafin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su matsawa kungiyar ta janye yajin aikin da ta shiga.
NAPTAN ta ce idan Buhari ya yi hakan ne gwamnati za ta iya sanin wani bangare ne na rahoton farfesan, gwamnatin za ta iya aiwatarwa.
Shugaban NAPTAN, Alhaji Haruna Danjuma ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da jaridar Vanguard a ranar Talata.
Hakan dai ya zo ne kamar yadda kungiyar ASUU ta bayyana kiran da shugaban kasar ya yi a matsayin tsarin tafiyar da mulki a mafarki ko irin tafiyar hawainiya wanda ta ce lamarin abin takaici ne matuka.
Dukkansu biyun, ASUU da NAPTAN suna maida martani ne ga kiran da Buhari ya yi a ranar Litinin cewa ’yan Nijeriya masu kishin kasa su matsa wa kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe watanni hudu tana yi.
Danjuma ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnatin tarayya taki duba rahoton kwamitin Briggs da aka mika mata sama da wata guda.