An fara hakar danyen mai a Nijeriya a shekarar 1957 inda aka fitar da jimillar gangar dayen mai 6,157,200 zuwa kasashen waje. Kamfanoni irin su Mobil, Tenneco, Gulf Oil (daga baya ta zama Chebron), Agip, da Elf an ba su lasisi tsakanin shekarar 1955 zuwa 1962 don bincike da hakowa.
An fara aikin tace mai a shekarar 1965 ta matatar mai ta Fatakwal (PHRC) wanda ke da karfin tace gangar mai 60,000 a kowace rana, wanda Shell BP ta gina a kan kudi kusan pan miliyan 12 (wanda yake daidai da naira biliyan25.6 a dandalin canjin kudi na MSN inda naira2,138 yake dai dai da pan1 na kudin kasar Birtaniya kamar yadda ta wallafa a watan Yulin 2024).
- Wakilin CMG Ya Zanta Da Shugaban Kasar Timor-Leste
- Yadda Aka Yi Taro Kan Alfanun Manufar Gyare-gyaren Sin A Sabon Zamani A Abuja
Matatar man ta Fatakwal (PHRC) da aka sabunta mai iya tace gangar mai 150,000 a kowace rana, ta fara aiki a shekarar 1985, wanda aka gina a kan kusan miliyan 850 na dalar amurka (wanda yake daidai da naira triliyan 1.3 , a dandalin kasuwancin kudaden kasar waje na FMDK inda naira1,576.66 yake daidai da dalar amurka daya kamar yadda ta wallafa a ranar 16 ga watan Yulin 2024).
An ba da gyaran matatun man a kan kudi dalar amurka biliyan 1.5 ga kamfanin da ake kira Tecnimont SPA.
Matatar mai ta Kaduna (KRPC) tana da karfin tace gangar mai 110,000 a kowace rana, wanda aka gina a shekarar 1976 a kan kudi dalar amurka miliyan 525 (kwatankwacin naira biliyan 827.9). A cikin 2021, gwamnati ta amince da ba da gyaran ta a kan kudin dalar amurka miliyan586 ga kanfanin da ake kira Saipem SPA.
Matatar mai ta Warri (WRPC) tana da karfin tace ganga125,000 a kowace rana,wanda aka gina a kan kudi kusan dalar amurka 478 (kwatankwacin naira biliyan753.8), ta fara aiki a shekarar 1978. A cikin 2021, gwamnati ta amince da gyaran ta a kan dalar amurka miliyan897 duk dai ga kanfanin Saipem SPA.
Wadanan matatun mai hudu da suke rufe yau kusan shekaru 12 ko fiye da haka, sun yi tsatsa, sun kuma rube a wuraren da suke cikin kufai ba tare da samar da digo daya na man fetur ba, har ila yau ba su taba yin amfani da karfinsu na tace ganga 445,000 a kowace rana ba a tsawon lokacin da aka kafa su.
Wani abun al’ajabi kuma da ke fitowa daga litattafan NNPC da Majalisar Dokoki ta kasa a fasalin wuri-na-gugan-wuri na Naira shi ne kamar haka:
Matatun man hudu da suka kasa fidda digon mai daya sun yi asarar naira biliyan162.2 a shekarar 2019 da kuma naira biliyan108.3 a shekarar 2020.
Albashi da sauran alawus da aka biya ma’aikatan KRPC sun kasance naira biliyan 26.02 a shekarar 2020 da naira biliyan34.5 a shekarar 2019.
Albashi da sauran alawus da aka biya ma’aikatan PHRPC sun kasance naira biliyan22.5 a shekarar 2020 da naira biliyan18.6 a shekarar 2019.
Albashi da sauran alawus da aka biya ga ma’aikatan WRPC sun kasance naira biliyan 20.51 a shekarar 2020 da kuma naira biliyan30.8 a shekarar 2019.
Rahoton mai da iskar gas na NNPC na watan Satumba na shekarar 2021 ya nuna jimillar gibin kudin da akasamu a hedikwatar NNPC da matatun mai hudu akan naira biliyan123.6.
Rahoton na watan Satumba na shekarar 2021 ya kuma nuna cewa hedkwatar NNPC ta samu kudaden shiga na naira biliyan11.1, yayin da aka kiyasta kudaden da ta kashe a kan naira biliyan17.06.
A cikin wannan rahoton na Satumba na shekarar 2021 matatun man sun samu kudaden shiga na naira miliyan 207 yayin da suka ci makudan kudade na naira biliyan 6.06.
Tallafin man fetur tsakanin Janairu zuwa Mayu ta shekarar 2022 ya kasance naira triliyan1.3.
Gyaran matatun mai tsakanin Janairu zuwa Mayun shekarar 2022 ya kasance kusan naira biliyan27.3.
Kididdigar fetur da NNPC ta fitar ta nuna cewa yawan man fetur da ake amfani da shi a kullum a Nijeriya ya kai lita miliyan 66.8.
A watan Afrilun shekarar 2023, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, ya ce a watan Afrilun 2023 zaa kammala aikin gyaran matatar mai na Fatakwal ,abu ne mai yuwuwa kuma kamfanin zai tace danyen mai ganga 60,000 nan da farkon shekarar 2024.
A watan Oktoban shekarar 2023, Majalisar Dattawa, a abin da suka gani na zagon kasa ne suka yi alkawarin binciken kudade naira triliyan 11.35 da aka kashe wajen gyaran matatun mai daga shekarar 2010 zuwa yau,kuma kwaliya bata biya kudin sabulu ba.
Sabanin abin da ke sama ne aka fara wani wasan kwaikwayo mai cike da rudani, wanda ya hada da Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC), da Hukumar Kula da Al’amuran Man da aka sarrafa ta NMDPRA, da kuma mai kula da al’amuran hako danyen mai ta NUPRC, Ma’aikatar Tarayya Albarkatun Man Fetur (FMPR), jami’an gwamnati marasa kishin kasa da ‘yan siyasa, jiga-jigan kamfanoni, da matatar Dangote mai son kawo sauyi a fannin makamashin kasa, ceto Nijeriya da ‘yan Nijeriya daga kangi.
Matatar man mai karfin tace ganga 650,000 a kowa ce rana, ana sa ran za ta rage dogaro da man fetur da ake shigowa da su Nijeriya. Amma duk da haka, tana fuskantan kalubale, ciki har da rashin samun danyen mai daga Nijeriya har sai ta je wasu kasashe, saboda yaudara a cikin gida da kuma bakin ciki.
Cin Amanar Kasa
Matatar dangote, wanda a ke ginawa akan kudin Amurka biliyan 20 (kwatankwacin naira triliyan31.3) wacce ta zarce kasafin kudin shakaran 2024 na Nijeriya tare da dukkan madakallan da ke tattare da kasafin kudin, yana fuskanta tasgaro duk da kuma fa’idar da za a samu, ayyukan ma’aikatan gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur ke yi, ya kara fitowa karara kasancewar wasu mutane da suka dukufa wajen durkusar da Nijeriya saboda muradunsu da ba shi da nasaba da muradun Nijeriya.
Saboda son rai na dan Adam, Kamfanin NNPC, a maimakon ya yi anfani da asusun ajiyar arziki na Sobereign Wealth Fund (SWF), sai ya sanar da ‘yan Nijeriya ta hanyar ba su bayanan bogi cewa ya sayi kashi 20 cikin dari na hannun jarin Matatar Dangote a kan dalar Amurka biliyan 2.76 ta hanyar ciniki mai suna Project Bison (wato Bauna a hausan ce). Sai dai wasu bayanan silili na baya-bayan nan sun nuna cewa hannun jarin bai fi kashi 7.2 cikin dari ba.
Har ila yau, sun ki sayar da danyen mai ga matatar ta Dangote, maimakon haka sun dukufa ne wajen kawo cikas ga ayyukan matatar, matakin da ke kawo cikas ga aikinta na samar da fetur domin biyan bukatun gida, da samar da ayyukan yi ga kusan mutane ‘yan Nijeriya 50,000, da kuma samun damar biyan bashin da ake bin matatar da kuma kawo dauki ga ‘yan Nijeriya.
Wani abun takaici shine duk jami’an da ke da hannun cikin wannan cin zarafin Nijeriya har yanzu suna zaune daram-dam-dam a kan kujerunsu da mukamansu maimakon fuskantar sakamakon aika-aikan su!
Wace irin kasa ce Nijeriya?
Labarin Kasar MaltaÂ
Amma jira, akwai kari. Malta, wani karamin tsibiri ne a baharmaliyan yankin turai, ya zama dan wasan da ba a zata ba a harkar man feturin Nijeriya a shekarar 2023, man da Nijeriya ta shigo da shi daga wata masana’antar hada man fetur (ba matatar mai ba fa!) daga Malta ya kai dalar amurka biliyan2.8 (kwatankwacin sama da naira triliyan 1). Wannan abun mamaki ne kwarai da gaske domin yana nufin ya karu da kashi 342 daga na shakarar 2013.
A cewar cibiyar da ke sa ido kan tattalin arzikin kasa (OEC), tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022, Nijeriya ta fi shigowa da tataccen man fetur daga kasashe da kamfanoni kamar haka:
1. Belgium- Ta shigo da man da ya kai dalar amurka biliyan 6.83 daga Total S.A, EddonMobil da PetroChina.
2. Netherlands-Ta shigo da man da ya kai dalar amurka biliyan 5.61 daga Royal Dutch Shell (Shell), Bitol Group, da Trafigura Group.
3. India- Ta shigo da man da ya kai dalar amurka biliyan 2.37 daga Indian Oil Corporation (IOC), Reliance Industries Limited (RIL), Bharat Petroleum Corporation Limited (BPCL).
4. Norway-Ta shigo da man da ya kai dalar amurka biliyan 1.64 daga Ekuinor ASA da Aker BP ASA.
5. United Kingdom-Ta shigo da man da ya kai dalar amurka miliyan923 daga BP (British Petroleum) da Shell (Royal Dutch Shell).
Tambaya:
Mece ce manufar masu rike da madafun iko? Me ya haifar da wannan karuwa? Me ya sa kasar Malta?
Cin Dunduniyar Nijeriya
Duk da cece-kucen da ake tafkawa, gwamnatin Nijeriyar dai ta yi kasa a gwiwa, inda ta mayar da martani na ko in kula da kin magance ayyuka da mu’amalar da hukumominta da jami’anta suka yi a-kai-a-kai wadanda ke kawo cikas ga ci gaban da kasa ke bukata.
An kafa NMDPRA a cikin Satumba, 2021 ta Sashe na 126 na Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA) 2021.Tsarawa da saka idanu, aiki a matsayin mai ba da shawara kan kasuwancin mai da sauransu, su ne aikin ma’aikatan.
A watan Yunin shekarar 2023 ta ba da sanarwar bai wa wasu kamfanoni 6 lasisin shigo da albarkatun man fetur zuwa Nijeriya, amma har yanzu ba a bayyana sunayen wadannan kamfanoni ba.
Bayan Cin Hanci da Rashawa  Â
Shin ya dace mai sa doka a harkan man fetur ya sa hannun jari? Shin Lekki Refinery Funding Limited (LRFL) na da izini kamar yadda Dokar Musayar kudaden Kasashen Waje ta tanada? Shin ‘Project Bison’ ya dace da Sashe na 11 (1) na Dokar Musanyar kudaden Waje? Shin NNPC ko LRFL sun saba wa sashe na 1(2) da sashe na 8 na dokar babban bankin Nijeriya na 2007? Sannan ko lokaci bai yi ba da ‘yan Nijeriya za su yi karatun ta natsu?
Rashin Tsari ko Sakaci Â
Mu yi la’akari da sassan da suka dace na Kundin Tsarin Mulki na 1999 na Tarayyar Nijeriya da sauran ka’idojin da suka jaddada kishin kasa, rikon amana, gaskiya, kulawa da kuma kiyaye muradun Nijeriya da ‘yan kasa: Ayyukan dan kasa (Sashe na 24), Bayanin kaddarori da lamuni (Sashe na 52), Rantsuwan Mambobi (Sashe na 54), Hakkokin ‘yan kasa na asali (Babi na IB). Sauran su ne: Ladabi na kasa (Sashe na 23), Kididdiga na Ofishin da’a da Dokar Kotu (Sashe na 3,15 da 18), Dokar Hukumar EFCC da kuma Dokar Hukumar hana cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) (Sashe na 6 da 26).
Tabbas! ‘Yan Nijeriya suna kallo kuma tarihi ba zai manta ba!