- Hukumar Ta Bayyana Hujjojinta
- Ta Gayyaci ‘Yan TikTok, Ta Ba Su 2,000 Na Data
- Koken Daliban Jami’a Kan Lamarin
- Rigakafin Dakile Barnar Ya Fi Farautar Mabarnatan –Masharhan
Cikin mako biyu da suka gabata, Hukumar Hisba ta Jihar Kano, karkashin jagorancin kwamandanta; Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta kaddamar da wani aiki da suka kira da ‘shirin tsaftace Jihar Kano daga harkokin badala’ da ke neman zama ruwan dare a jihar.
Yanzu haka, kamen da hukumar ta kaddamar ya hada da otal- otal, wuraren cin abinci, wasu daga cikin gidajen dalibai mata da masu zaman kansu da kuma sauran wuraren shakatawa.
Da yake yi wa manema labarai karin; Sheikh Daurawa ya bayyana cewa, aikin da ake yi na cikin kudirin da aka kafa hukumar dominsa.
- Hisbah Ta Yi Wa Mutum 4,000 Rajista Da Ke Son Gwamnatin Kano Ta Aurar Da Su
- Batun Yadda Samari Ke Barin Taimakon Iyaye Su Kashe Wa ‘Yan Mata Kudi
Ya ce, “aikin Hisba shi ne yin umarni da aikin alhairi da kuma hani da mummunan aiki. Don haka, kamar yadda aka sani musulunci ya haramta ire-iren wadannan abubuwa da wasu rukunin matasa maza da mata ke aikatawa, wadanda Allah ke fushi da su. Lamarin na neman zama wata annoba da ke neman addabar al’ummar, saboda haka yanzu wannan hukuma ta sake sabunta shirinta na tsaftace Kano daga ire-iren wadannan ayyuka na badala. Kamar yadda muke samun rahotanni daban-daban, na yadda matasa ke neman mayar da Kano wani sansani haduwa, domin gudanar da harkokin badala; wanda ko kadan wannan hukuma ba za ta taba sanya idanu tana kallo ana aikata abubuwan da Allah ya hana ba”, in ji shi.
Har ila yau, Hukumar Hisbar, ta gayyaci masu amfani da dandalin shafin sada zumunta na Tiktok, zuwa hukumar ofishinta da ke kan titin Sharada a Kano. Inda Kwamnadanta ya bukaci kowa ya yi kokarin gyara halayensa tare da kyautata tarbiya, domin zama mutane nagari.
Sannan, ya nusasshe su da cewa, a nan gaba su ne iyaye masu fada a ji, don haka akwai bukatar su daina yin abubawan da ba su dace ba, domin yin hakan yana zubar da kima da kuma jawo fushin Allah. A karshe sai ya raba wa kowannensu naira dubu biyu-biyu, domin sa data (kudin shiga intanet.
LEADERSHIP Hausa ta ji ta bakin wasu Kanawa kan wannan aiki da Hisba ke yi, inda suka bayyana ra’yoyinsu.
Daya daga cikinsu, Malam Muhammad, ya bayyana cewa ko shakka babu Jihar Kano a halin yanzu ta tara wuraren shakatawa, kamar yadda ta tara kananan mata wadanda suke yawon ta-zubar. “Ina goyon bayan ayyukan Hisba na yaki da barna da lalata a Jihar Kano, amma a nawa ganin bin hanyoyin dakile barnar ya fi a rika farautar mabarnatan.”
Ya ce, idan har Gwamnatin Jihar Kano za ta rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba, “ina ganin abu ne mai matukar sauki a rufe dukkanin wuraren barnar a wannan jiha. Domin kuwa, idan aka yi la’akari da yanayin yadda mata ke tururuwar shigowa Kano, suna kama gidajen haya suna shaye-shaye gami da lalata, ba karamin abin tsoro ba ne.
“Duk da cewa, mafi yawansu suna zuwa ne domin shiga fim din Hausa, amma me zai hana gwamnati ta hada kai da masu unguwanni a kira dillalan gidaje a hana su bai wa ire-iren wadannan mata masu zaman kansu hayar gidaje?
“Haka zalika, me zai hana hukumar tace fina-finai ta wajabta wa kowace yarinya samun sahalewar iyayenta? Sannan, me zai hana a rika kama duk wani Furodusa ko Daraktan da ya kara sa yarinya a fim ba tare da gwamnati ta yi mata rajista ba? Me zai hana a hukunta duk wani dan fim da aka samu yana ajiye mata a ofis ko sitidiyo dinsa?”
Shi ma da yake nasa tsokacin, Malam Salihu Murtala Hotoro, ya yi kira ne ga Hisbah ta gyara salon yadda take yin kamen matan kamar yadda wasu suka rika yin korafin cewa an ci zarafinsu, na yi musu daukar amarya. “Babu shakka, duk mutumin kirki zai goyi bayan hana ayyukan badala domin guje wa afka wa fushin Ubangiji da kuma yaduwar cututtuka. Sannan kuma, a duk inda aka samu yawaitar mata masu zaman kansu, manyan laifuka na kara yawaita tare da kyankyashe sabbin masu laifi.
“A irin wannan hali da sabon salon da Hukumar Hisba ta dauka, na kokarin kakkabe masu yawon ta zubar. Su ma dalibai na cikin fargaba da hadari a Kano. Ko shakka babu, salon da Hisba ke amfani da shi ya saba wa musulunci, ” domin kuwa bai kamata a zura ido ana cin zarafin mutane da sunan gyara ba.
“Ko kadan, bai kamata Malamin da ya yi shuhura wajen bayar da fatawa tare da tarbiyya ya bari ko ya bayar da umarnin cin zarafi ta hanyar keta mutunci da tozarta Dan’adam da sunan gyara ba”, in ji shi.
A wani bangaren kuma, bakin dalibai mata da ke karatu a Jihar Kano na cikin fargaba, sakamakon yadda ake zargin Jami’an Hisbar da kutsawa har gidajen kwanansu suna kamo su da sunan masu aikata badala, “har cikin gida suka balla kofa suka afko suka kama ‘yan’uwanmu dalibai suka tafi da su”, a cewar wasu daga cikin daliban Jami’ar Bayero da aka zanta da su.
“Tun a daren da aka kama su; muke bin diddigi amma sun ki sakin su. Kodayake, sun kai su ofishin ‘yansanda; amma ga dukkanin alamu DPOn ya ki rubuta musu takardar shigar da kara da suka nema, DPOn ya ce bai san laifin da zai rubuta mutanen sun aikata ba, sannan kuma ba shi ne ya sa aka kamo su ba”. Daga bisani, an ruwaito Hukumar Hisbar ta yi amfani da motoci ta kwashe wadanda ake zargi da bidalar zuwa hedikwatarta, domin gurfanar da su a gaban kotu.” In ji daya daga cikin dalibai mata da aka zanta da su.
Sannan sun bayar da misalai da wasu daga cikin ‘yan matan da aka kama a wasu daga cikin wuraren cin abinci da ke unguwar masu hannu da shuni a Unguwar Nasarawa, inda da dama daga cikin wadanda aka kaman suke nuna cewa, su dalibai ne wadanda suka zo sayen abinci.
Sai dai kuma, akwai wadanda suke ganin, daliba ‘yar makaranta ta tashi zuwa Nasarawa sayen abinci, mummunar dabi’a ce, inda suka bukaci iyaye su sake nazarin sanin dabi’un ‘ya’yansu a wuraren da suke karatu. Haka nan, su ma Hukumomin Makarantu a kwai babban kalubale a gabansu; kasancewar yaran nan amana ce a hannunsu.
Hakazalika, wasu masu sharhi, na ganin wannan terere da Hisba ke yi a kan wadanda ta kaman, a matsayin keta dokar musulunci da kuma ita kanta dokar da ta kafa hukumar.
Guda daga cikinsu, Ali Jamilu ya yi bayanin cewa, “sumamen da Hisba ta yi na kame da bulala tare da yin kwarmato ga ‘yan jarida, tozarci ne ga Dan’adam; wanda hakan ya saba wa musulunci da karantarwar Annabi Muhammadu (SAW). Sannan kuma, babu a inda dokar da ta kirkiri hukumar ta ba su damar yin hakan”.
Ya kara da cewa, “kamata ya yi Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, ya ja hankalin Hukumar Hisbar, domin sanin matsayinsu a dokar da ta kirkiri hukumar.
“Har wa yau, muna bayar da shawara a rika yin aiki da lura tare da bin doka da oda, ba wuce gona da iri ba; wanda hakan ya saba wa dokokin musulunci da ake ikirarin ana aiki da su”, in ji Jamilu.
Bugu da kari, wasu daga cikin Malaman Kano; sun jinjina wa kokarin hukumar ta Hisba, bisa wannan gagarumin aiki da ta dauko. A cewar tasu, haka ya kamata hukumar ta yi domin kuwa a kullum lamarin kara tabarbarewa yake yi.
…. Hisba Ta Kori Jami’inta Bisa Zargin Karbar Cin Hanci Daga Masu Otal A Kano
A halin da ake ciki kuma, Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kori wani jami’inta da ake
zargi da yi mata zagon kasa a kokarin da ta ke na yaki da badala da miyagun ayyuka a Jihar Kano.
Kwamamdanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka alokacin wata ganawa da Manema labarai, ranar Talatar da ta gabata.
“Mun Kori Mataimakin Sufuritandan Hukumar Hisba, DSH tare da neman sa ruwa a jallo domin damke shi. Kasancewar yana hada baki da ma’aikatan otal-otal domin hana Jami’an Hisba kai farmaki otal dinsu cikin aikin da hukumar hisba ke yi a halin yanzu.
“An bayyana mana yadda ake ba shi kudi domin hana Jami’an Hisba isa otal otal dinsu. Akwai guda cikin masu otal din da ya tambaye mu, me muke bukatar su yi mana domin ba mu gudunmawa. Inda muka sanar da shi wannan aiki ne da gwamnati ta dora mana domin aiwatar da shi. Daga nan sai ya ce, ya za su bai wa Hisba kudi sannan kuma a juya masu baya tare da kawo farmaki otal dinsu?”.
Sheikh Daurawa ya kara da cewa, yanzu haka ma akwai sauran mutane biyar daga cikin jami’an na hisba da ake gudanar da bincike a kansu.
“Ba ma kai farmaki har sai mun samu korafi daga al’umma wanda akalla mutum biyar suka rattaba hannu a kai. Sannan kuma muna fara gudanar da binciken sirri ta hanyar tura jami’anmu na farin kaya domin tabbatar da gaskiyar bayanan da muka samu, daga nan kuma sai mu sanar da babban jami’in ‘yan sandan yankin (DPO) domin samun kariya tare yin aiki tare da kotu.” In ji Sheikh Daurawa.