Yayin zama karo na 3 na kwamitin tabbatar da da’a da ladaftarwa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis na kasar Sin na 20, wanda ya gudana a jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a jaddada kokarin samun nasara a yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce yaki ne dake bukatar juriya da dauriya.
Yaki da cin hanci da rashawa ya zama tamkar wata alama dake wakiltar kasar Sin da na dade da saninta tun kafin shigowata kasar. Akasari, al’ummar Nijeriya kan yi kwatance da kasar Sin a duk lokacin da aka samu wata badakalar cin hanci dake bukatar ladaftarwa, don haka na taso, na kuma kwan da sanin cewa, kasar Sin kasa ce da ba ta lamuntar wannan mummunar al’ada.
- Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa A Harkokin Duniya
- INEC Ta Shirya Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihar Kano
Abun burgewa shi ne, duk da suna da fice da ta yi a bangaren yaki da cin hanci da rashawa, har yanzu kasar Sin ba ta yin kasa a gwiwa wajen tabbatar da ba a mayar da hannun agogo baya ba, kamar yadda muka ji, muka kuma gani a jawabin shugaba Xi Jinping na jiya.
A ko da yaushe, kasashenmu masu tasowa kan yi buri da ikirarin neman ci gaba mai inganci da karfafa tattalin arzikinsu, sai dai, babban abun dake ci musu tuwo a kwarya shi ne, cin hanci da rashawa. Wannan matsala ce da ta yi katutu a kasashenmu, domin kowa ya samu dama, to neman gina kansa yake maimakon kasa. Wannan dalili kadai, ya sa muka bambanta da kasar Sin da kuma hanyar da ta dauka na raya kanta.
Muddin kasashenmu na son taka matakin da kasar Sin ta kai a duniya, to dole ne su zage damtse su kuma dauki batun yaki da cin hanci da rashawa da muhimmanci, ta yadda babu wanda zai tsira daga fushin hukuma idan aka same shi da laifi. Haka kuma, a yi kokarin datse matsalar tun daga tushe da kuma kokarin ganin an cusa kyakkyawan akida da kishin kasa a zukatan al’umma.
Kamar yadda Shugaba Xi ya bayyana, yaki da cin hanci, aiki ne dake bukatar hakuri da juriya, haka kuma ba shi da wa’adi, sannan yana bukatar kyakkyawan kuduri na shugabanci. Wadannan dabaru ne da ya kamata kasashenmu dake burin koyi da kasar Sin ya kamata su nazarta, su kuma dauka, domin ta hakan ne kadai, za a kai ga matakin da ake buri da samun al’umma mai kyakkyawar dabi’a da kishin kasa kamar kasar Sin.