Kudurin kawar da talauci na cikin muhimman bukatun bil adama da tun kaka da kakanni ake hankoron cimma nasararsa. Kuma a duniyar yau, akwai mutane da yawansu ya haura biliyan guda dake rayuwa cikin kangin talauci. Yayin da duniya ke kara dukufa wajen shawo kan wannan matsala, kasar Sin ta yi namijin kokari, wajen samar da damammaki na karfafa gwiwar al’ummun duniya don cimma kyakkyawar rayuwa.
A cikin gida, kasar Sin ta yi nasarar tsame sama da al’ummunta miliyan 800 daga kangin talauci, ta kuma yi nasarar cimma kudurin samar da ci gaba mai dorewa, wanda ke cikin ajandar wanzar da ci gaba ta MDD ta nan da shekarar 2030, tun ma kafin cikar wa’adin ajandar.
- Jam’iyyar Labour Ta Yi Mummunar Asara, Ƴan Majalisa 5 Sun Fice
- Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da CBN Daga Sallamar Ma’aikata 1000
Hakan nen ma ya sanya masharhanta da dama ke jinjinawa kwazon kasar a fannin yaki da fatara, musamman ta hanyar dunkule dabarun bunkasa ci gaban tattalin arziki, da manufofin inganta walwalar al’umma. Ta hanyar tsara manufofi daidai da yanayin da ake ciki a sassan kasar daban daban, kasar Sin ta tabbatar da ganin matakan yaki da fatara sun magance takamaiman matsalolin al’ummu mabambanta.
Wannan wani tsari ne da ya taimaka matuka, wajen sauya yanayin wasu sassan kasar da a baya suka yi fama da matsanancin kangin talauci, har ma hakan ya zama misali, kuma abun koyi ga kasashen duniya da dama a wannan fanni.
Ga misali, a kasar Rwanda, fasahar noman ciyawar Juncao da kasar Sin ta gabatar, ta taimakawa manoman yankunan karkara, da fasahar noman nau’o’in tsirrai kamar lemar kwado da ciyayin kiwata dabbobi. Hakan ya baiwa manoman kasar damar samun karin kudaden shiga, da samar da yalwar abinci, da tabbatar da ingancin muhalli. Yanzu haka wannan fasaha ta noman Juncao ta shiga kasashen nahiyar Afirka sama da 40, inda a ko ina ake cin gajiyarta.
Baya ga batun yaki da fatara, kasar Sin ta gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” ko BRI, wadda da hadin kan sauran kasashe musamman masu tasowa ake samar da ababen more rayuwa, da raya ilimi da kiwon lafiya. Ko shakka babu wadannan ayyuka sun samar da guraben ayyukan yi, da hade sassa mabambanta wuri guda, da yaukaka ci gaban kowa da kowa, tare da taimakawa wajen tsamo dubban jama’a daga kangin fatara.
BRI ta riga ta hallara kasashe da yankunan duniya sama da 160, kana ana aiwatar da manufofinta masu inganci tare da sama da kasashen duniya 150, kuma karkashinta an shigar da kudaden da yawansu ya doshi dalar Amurka biliyan 20, don gudanar da ayyukan raya kasashe sama da 1,100. Wanda hakan ya zamo wata kyakkyawar dama ta ingiza ci gaban kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.