Yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar kalubale ne ga kasashen Afirka, amma kuma dama ce gare su, ta la’akari da yanayi mai armashi da huldar Afirka da Sin ke ciki, musamman ma ta fuskar cinikayya. Wannan ya riga ya zama ra’ayin bai daya na mutanen Sin da na kasashen Afirka.
Kwanan baya, kungiyar ciniki ta duniya WTO ta gabatar da rahoton hasashen yanayin ciniki na duniya, inda ta ce matakin karbar karin harajin kwastam da kasar Amurka ta dauka, da sauran manufofin kasar marasa tabbas, za su iya haddasa raguwar cinikin kayayyaki da ta kai kaso 1.5% a duniya, lamarin da zai illata kasashe marasa karfin tattalin arziki, wadanda ke dogaro kan sayar da kayayyaki ga kasashen ketare.
- Za A Yi Jana’izar Fafaroma Francis A Ranar Asabar A Vatican
- Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
Yayin da Ngozi Okonjo-Iweala, babbar darektar kungiyar ta WTO ke gabatar da wannan rahoto, ta ambaci misalin kasar Lesotho. A matsayin daya daga cikin kasashen dake dogaro kan fitar da kayayyaki zuwa waje, kasar Lesotho ta fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 237 a duk shekara ga kasar Amurka, wadanda yawancinsu lu’u-lu’u, da yadi mai kwari ne. A cewar mujallar Foreign Policy ta kasar Amurka, ta la’akari da raunin tattalin arzikin kasar Lesotho, inda matsakaicin kudin shigar duk mutum daya bai wuce dala 975 a shekara daya ba, kudin harajin kwastam na kaso 50% da kasar Amurka ta yi shirin kakaba wa kasar, zai iya haifar da barna ga tattalin arzikinta.
Sai dai a hakika, ba dole ne kasar Lesotho, da sauran kasashen Afirka su mika wuya ga kasar Amurka, don ta ci zalinsu yadda ta ga dama ba. Kamar yadda Charles Olunaiju, wani masanin kasar Najeriya, ya rubuta a cikin wata makalarsa da jaridar Vanguard ta wallafa, kasar Amurka ba za ta samu biyan bukata a yakin ciniki da ta tayar ba, saboda dunkulewar duniya sakamakon dimbin cinikin da ake yi tsakanin kasashe daban daban, da hadewar sassan duniya da cudanyar mabambantan al’adu, wadanda aka samu bisa tushen ci gaban fasahohi, sun haifar da wani yanayi mai armashi da ba za a iya sauya shi ba.
Mista Olunaiju ya kara da cewa, a matsayin wata dabarar tinkarar rikici, kasashen Afirka za su iya amfani da tsarin yankin ciniki mai ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA) wajen mai da nahiyar dunkulallun kasuwanni, da babban yankin da ake zuba masa jari, ta yadda za a ba kasashen Afirka damar aiwatar da Ajandar Raya Kasa ta 2063 yadda ake bukata. A sa’i daya kuma, kasar Sin, bisa matsayinta na abokiyar hulda mafi muhimmanci a fannin cinikayya ga kasashen Afirka, za ta samar da taimako ga nahiyar Afirka a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya, da walwala, in ji Mista Olunaiju.
Sa’an nan, a nasa bangare, Dennis Mwaniki, shahararren mai nazarin manufofin hukumomi dan kasar Kenya, yana da ra’ayin iri daya dangane da yakin cinikin da kasar Amurka ta kaddamar, inda ya ce, matsin lamba da Amurka ta dora wa kasashen Afirka zai sa su kara karkata ga kasar Sin, da sauran manyan tattalin arziki dake tasowa. Saboda yayin da kasar Amurka ke rufe kofarta, sauran kasashe sun ba da karin damammakin kulla huldar ciniki, wadda za ta samar da sakamako mai gamsarwa. Sabanin matakin kasar Amurka na karbar karin harajin kwastam, kasar Sin ta yafe wa kasashe masu raunin tattalin arziki harajin kwastam, da ba su sauran tallafi da gatanci, lamarin da ya janyo hankalin dimbin ‘yan kasuwan kasashen Afirka ga kasuwannin kasar Sin mai yawan al’umma da ya kai biliyan 1.4. Mista Mwaniki ya jaddada cewa, “Wannan tsari zai tabbatar da moriyar kowa, ba kamar manufar da Donald Trump ya daukaka ta Cin Moriya daga Faduwar Wani ba.”
Ban da haka, jawabin da jakadan kasar Sin a Najeriya Yu Dunhai ya yi, a birnin Abuja a kwanan baya, ya zama mai goyon bayan maganganun da masanan kasashen Afirka suka fada, inda jakadan ya ce, ya kamata a kalli yakin ciniki a matsayin wata damar karfafa huldar hadin kai tsakanin kasashen Sin da Najeriya, gami da tsakanin Sin da kasashen Afirka baki daya. Yanzu kasashen Afirka na kokarin farfado da tattalin arzikinsu, saboda haka suna bukatar tsarin ciniki mai ‘yanci da ya shafi bangarori daban daban, da wani muhallin kasuwanci da ake iya hasashen yanayinsa na nan gaba. Yayin da kasar Sin a nata bangare take dukufa wajen bude kofarta ga kasashen ketare, da kokarin taimakon kasashen Afirka wajen raya kansu a kai a kai, matakan da ke da muhimmanci ga yunkurin saukaka yanayin rashin tabbas da ake fuskantar sakamakon yakin ciniki.
Sai dai wadanne matakai ne za a iya dauka don tinkarar yakin ciniki? Za mu iya ci gaba da daukar misalin kasar Lesotho, inda kayayyakin da take fitarwa kasar Amurka, idan Amurka ba ta so, to, za a iya bin shawarar Madam Ngozi Iweala, wadda ta ce sai a sayar da su ga sauran kasashen dake nahiyar Afirka. Ban da haka, kasar Lesotho za ta iya hadin gwiwa da kasar Sin wajen inganta tsarin masana’antu, ta yadda za ta lalubo sabuwar damar ciniki. Ganin yadda kasar Sin ta zama kasa ta farko da ta kulla huldar hadin kai bisa manyan tsare-tsare tare da Lesotho, kana adadin cinikin da ake yi tsakanin kasashen 2 ya riga ya karu zuwa dala miliyan 150 a bara.
Sinawa kan ce, “Dabara ta fi matsala yawa.” Mu yi kokarin tinkarar kalubale, ta yadda za a iya mayar da shi damar raya kai. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp