Matashin dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lamine Yamal ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi na tsawon shekaru shida 6 tare da Barcelona, hakan zai sa ya cigaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2031, in ji wata sanarwa da zakarun na kasar Sifaniya suka fitar a ranar Talata.
Yarjejeniyar Yamal da ta gabata za ta kare ne a shekarar 2026 kuma kulob din na Catalan ya ba shi fifiko a wannan bazarar, daraktan wasannin kungiyar Deco ya ce tsawaita kwantiragin Yamal shi ne “sa hannu mafi kyau” da kulob din ya yi a cikin shekaru, yayin da shugaba Joan Laporta ya ce dan wasan mai shekaru 17 ya cancanci karramawa ta musamman.
A cewar jaridar ESPN, sabuwar yarjejeniyar ta hada da karin albashi mai tsoka, kwatankwacin muhimmancin da koci Hansi Flick zai bashi sai kuma dimbin kunshin banas, sannan kuma akwai kyautuka na musammman da aka tanada ma dan wasan na kasar Sifaniya muddin ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon D’or.
Yamal ya fara bugawa Barcelona wasa tun yana dan shekara 15 a shekara ta 2023 kuma cikin sauri ya zama daya daga cikin fitattun ‘yan wasa a duniya, inda ya taimakawa kasar Sifaniya lashe gasar cin kofin nahiyar turai a bazarar da ta gabata kuma ya taka rawar gani yayin da Barça ta lashe kofin Laliga, Spanish Super Cup da Copa Del Rey a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp