Gwamnatin Jihar Kaduna ta zargi ‘yan adawa da dana wa Ministar Harkokin Mata, Barista Uju Kennedy-Ohanenye tarko yayin da suka kitsa mata cewa, akwai rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekara 20 a tsakanin Hausa/Fulani da kabilun Koro da Gbagyi a yankin Karamar Hukumar Kagarko da ke kudancin jihar.
Gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa domin mayar da martani kan wasu rahotonni da kafafen yada laba-rai suka fitar da ke cewa, ministar ta yi wani taron sulhu da wasu kabilun karamar hukumar ta Kagarko domin wanzar da zaman lafiya tsakaninsu.
- Gwamna Lawal Ya Nanata Bukatar Hadin Kai Tsakanin Hukumomin Tsaro
- Gwamna Radda Ya Yi Allah Wadai Da Hare-haren ‘Yan Fashin Daji A Jihar Katsina
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, inda ta bukaci al’ummar Jihar Kaduna da sauran ‘Yan Nijeriya su yi watsi da kalaman da suka ce babban kuskure ne mai hadari da wasu kafafen yada labarai suka yada.
Gwamnatin ta yi takaicin yada irin wadannan labaran ba tare da tantance gaskiyar lamarin ba wanda a cewarta, ka iya haifar da rudani da tada zaune tsaye a Karamar Hukumar Kagarko.
“Domin kauce wa shakku, ya kamata jama’a su lura cewa, babu wani rikici a Karamar Hukumar Kagarko. Hasali ma, karamar hukumar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali na tsawon shekaru kuma har yanzu tana daya daga cikin kananan hukumomin jihar da ke zaune cikin kwanciyar hankali.
“Gamnatin jihar Kaduna ta samu sahihan rahotanni da ke nuni da cewa, ‘yan babbar jam’iyyar adawa ne suka kitsa makircin da nufin zamba ga gwamnatin tarayya, inda suka dana wa ministar harkokin mata tarko kuma ta fada ta hanyar bijiro mata da labarai marasa tushe na rashin jituwa da rikici a tsakanin kabilun da ke Karamar Hukumar Kagarko.
“Ministar, ba tare da tantance ikirarin nasu na bogi ba, kuma ba tare da tuntubar jami’an Karamar Hukumar Kagarko da na Gwamnatin Jihar Kaduna ba, duk da kasancewarta Lauya, amma ta ta fitar da sanarwar alkawurran filayen noma ga mutanen yankin da ke rikici da juna.
In ba a manta ba, a ranar 2 ga watan Nuwamba ne, Ministar harkokin Mata ta kasa, Barista Uju Kenne-dy Ohanenye ta bayyana a shafin sada zumunta na D da akafi sani da twitter (@BarrUjuKennedy), inda ta ce, “Wannan babbar nasara ce da ma’aikatarta ta samu na samar da zaman lafiya a tsakanin al’umomin Koro da Hausawa da Fulani da ke rikici a Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, domin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru 20 ana yi. Ma’aikatar za ta samar da fili Eka 100 don yin noma na zamani a yankin, wanda hakan zai taikamaka wa mutanen yankin su kaunaci juna maimakon ci gaba da yakar juna.”
A rahotannin da wasu gidajen talabijin na kasa suka yada, an ga ministar tare da wasu tsirarun mutanen da suka zama wakilan kabilun a wurin taron, suna bayani a kan cewa “bisa wannan tallafi da alheri da kika zo mana da shi, komai ya wuce, za mu zauna lafiya.”
Har zuwa lokacin hada wannan labari dai, minister ba ta ce uffan kan lamarin ba ko wata sanarwa daga ma’aikatarta.