A ranar Juma’a 16 ga watan Agusta aka fara gasar firimiyar Ingila, gasar da ake ganin za ta iya samar da canji a bangaren kungiyar da za ta iya lashe gasar, bayan shafe kakar wasa hudu kungiyar Manchester City tana lashe gasar a jere.
A baya dai an yi zakakuran ‘yan wasa daga nahiyar Afirka da suka haska a gasar ta Ingila irinsu Didier Drogba da Yaya Taure da Yakubu Ayegbeni da Machael Essien da Nwanko Kanu da Jay-Jay Okocha da sauransu.
Sai dai kawo yanzu akwai da yawa daga cikin manyan ‘yan wasa daga Afirka da suke buga kwallo a gasar da suka hada da Mohammad Salah da Muhammad Kudus da Adingra da sauran ‘yan wasan da suke buga wasa a wannan kakar a Ingila.
Muhammad Salah
Dan wasan kasar Masar, Mohamed Salah zai iya bugan kirjinsa ya ce shi ne kan gaba cikin ƴan kwallon Afirka da suka taba buga gasa a Gasar Firimiyar Ingila amma kuma yadda kyaftin din na tawagar Masar ke buga wasa, za a iya cewa kakar bara ba ta yi masa kyau ba, inda ita kanta kungiyar Liberpool ta gaza wajen yin katabus.
Kwallaye 18 da ya zura ne a kakar bara, biyar a bugun fanareti- shi ne adadi mafi kankanta da ya zura tun zuwansa kungiyar a shekarar 2017, duk da cewa ya taimaka an zura kwallo sau 10 sannan ciwo ya hana dan wasan mai shekara 32 buga Gasar Kofin Afirka ta 2023, da kuma wasu wasanni, sannan abubuwa sun kara cabewa a lokacin da aka hango shi yana musayar yawo da kocinsa na wancan lokacin, Jurgen Klopp.
Amma bayan Klopp ya bar Liberpool, da kuma kasancewar saura masa shekara 1 a kwantiraginsa, sai aka fara hasashen cewa Muhammad Salah zai bar Liberpool, har aka fara cewa zai koma Saudiyya da buga wasa.
Ana cikin wannan ne Salah ya sanar da cewa zai ci gaba da zama a Liberpool, inda ya ce zai fafata domin gyara abubuwan da suka faru da kungiyar a kakar bara, inda ta kare ba tare da lashe wani kofi ba. Sai dai kawo yanzu ba a sani ba ko zai ci gaba da kasancewa a kungiyar karkashin sabon kociyan kungiyar Arne Slot?
Yiwuwar sauya salon wasan kungiyar, daga yawan kai hare-hare, zuwa tsarin da ake kira da na ‘Dutch’ na (rarraba kwalo daga gida zuwa tsakiya, sannan a jefa wa dan wasan gaba) watakila zai iya yi masa dadi kasancewar shekarunsa sun fara ja amma sai dai akwai masu ganin cewa tsarin zai iya kawo cikas ga Salah, wanda ya fi son kwallon zurawa da gudu.
Liberpool ba ta dauko wani sabon dan kwallo ba, wanda hakan ya sa ake tunanin har yanzu shi ne zai ja ragamar kungiyar a kakar bana amma abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya da dan wasan a kakar bana, da kuma ganin ko kungiyar za ta sabunta kwantiraginsa a karshen kakar bana.
Yankuba Minteh
Daya daga cikin cinikin ‘yan kwallo da aka yi a kakar bana shi ne na dan wasan kwallon Gambiya, Yankuba Minteh, wanda a kakar bara ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord a karkarshin mai koyarwa Arne Slo Liverpool.
Dan wasan mai shekara 20 ya koma Newcastle United ne daga kungiyar Odense ta Denmark a Yunin bara a kan kudi kusan fan miliyan biyar, amma kungiyar ta tura shi aro domin ya kara gogewa. Sai dai bayan ya jefa kwallo 10 a wasanni 27 a gasar Netherland, sai Eberton da Lyon da Borussia Dortmund suka fara zawarcinsa, amma Brighton ce ta samu nasarar dauko shi a kan £30m.
Cewa zai nuna bajinta, kamar yadda Saintfiet ya bayyana ya yi daidai, kasancewar Minteh matashin dan wasa ne mai gudu, da iya zara da iya zura kwallaye wanda hakan yasa ake ganin magoya bayan kungiyar Brighton za su yi fatan ganin ya fara kafar dama.
Thomas Partey
Lokacin da Arsenal ta kashe £ 45m ($57.8m) a kan dan wasa Thomas Partey a watan Oktoban shekara ta 2020, an sa rai sosai cewa zai kara wa tsakiyar kungiyar karfi amma duk da buga wasanni 95 a Gasar Premier a kaka hudu da ya yi, har yanzu dan wasan na Ghana bai nuna bajintar da aka yi zato ba, saboda yawan jin rauni.
A yanzu da ya rage saura shekara daya a kwantiraginsa, idan har zai iya taimakon Arsenal ta lashe Gasar Firimiyar Ingila a karon farko bayan shekara 21, hakan zai iya zama masa ban-kwana mai kyau a rayuwarsa ta kungiyar.
Pape Matar Sarr
Matashin dan wasa Matar Sarr yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka haska a gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2023 kuma tun a kakar bara da sabon kocin Tottenham Postecoglou ya fara aiki ne aka fara ganin alamar zai yi amfani da dan wasan na tsakiyar Senegal din.
Duk da raunin da ya samu a tsakiyar kaka a lokacin da ake hutun Afcon, dan wasan mai shekara 21 ya buga wasa 27 a Premier a kakar 2023 zuwa 2024 kuma ana kallonsa a matsayin daya daga cikin zaratan ‘yan wasan wannan zamanin a kasarsa, zai iya kara wa Tottenham din karfi?
Dan wasan na Senegal, a kakar bana dai za a zura ido a gani irin rawar da zai taka ne a kungiyar ta Tottenham kuma ana ganin yana daya daga cikin ‘yan wasan da za su taimakawa Tottenham wajen cimma burinta na kammala gasar firimiya a mataki na ‘yan hudun farko.
Kakar bara ce kaka ta biyu a tarihin Premier da kungiyoyin uku da suka shigo gasar suka yi karkon kifi, inda dukansu suka koma a Gasar Championship a shekarar kuma yanzu Ipswich Town da Leicester City da Southampton za su dage wajen ganin sun kauce wa irin abin da ya faru da kungiyoyin Burnley, Luton da Sheffield United.
Kungiyar Leicester City za ta dogara ne da ‘yan wasan Afirka da ke kungiyar, sannan sun yi farin cikin sabunta kwantiragin da fitaccen dan wasan tsakiyar Najeriya Wilfred Ndidi ya yi. Sannan dan wasan Zambia Patson Daka da dan wasan gaban Ghana Abdul Fatawu ne suka jagoranci gaban kungiyar a kakar bara, inda su ukun suka zura kwallo 12 a Gasar Championship.
Kungiyar Ipswich ta dawo Premier bayan shekara 22, inda yanzu kyaftin dinta shi ne Sam Morsy dan kasar Masar, sannan akwai Adel Tuanzebe dan kasar DR Congo a cikin ‘yan wasanta sanan ita ma Southampton tana da zaratan ‘yan wasan Afirka, inda ake sa ran dan Najeriya Joe Aribo zai nuna bajinta a kungiyar sosai a bana.
Kwanan nan ne kocin Southampton, Russell Martin ya bayyana dan wasan gaban Najeriya wanda ya yi kakar bara a kungiyar Trabzonspor a matsayin aro, a matsayin na daban bayan wasannin atisaye da suka buga.
Amma har yanzu dan wasan Ghana Kamaldeen Sulemana bai gama warware ba daga raunin wata 18 da ya yi, inda yanzu haka aka tabbatar ba zai buga wasansu na farko na sabuwar kakar ba.