Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun banka wuta wa fadar basaraken gargajiya na Ndia Ndia Iche Arondizuogu da ke karamar hukumar Ideato ta arewa a jihar Imo, Eze Kanu Ikenolu.
Farmakin ya janyo wa al’ummar Masarautar shiga matsanancin firgici da har hakan ya sanya suka yi ta gudun neman tsira.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, isar maharan zuwa fadar ke da wuya suka jefa abubuwan fashewa da hakan ya janyo tashin wuta da ya kona gidan da motocin da ke ajiye a harabar wurin.
Wakilinmu ya gano cewa kewayen basaraken da gidan sarkin da fadarsa dukka sun lalace sakamakon farmakin.
Ganau sun shaida cewar, kadarorin miliyoyin naira ne ‘yan bindigar suka barnata.
Ganau din suka ce, “Masarautar mai martaba Eze Ikenolu, Eze of Ndia Iche Arondizuogu, ya kasance a mamaye da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, yanzu haka mutane sun arce zuwa dazuka.
“Kafin yanzu, babu wani yunkuri da ‘yansanda suka yi a kan harin masarautar HRH Eze Kanu na Ndianiche Arondizuogu, yayin motoci, gida, kadarori da suka zarce na miliyoyin duk sun lalace.”
A lokacin da aka tuntubi jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansandan jihar Imo, Henry Okoye, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa an kaddamar da bincike kan harin kuma ta bada tabbacin za a cafko masu hannu a wannan danyen aikin.