Wasu ‘yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a yankin Heipang, da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi, ta jihar Filato da safiyar Laraba, inda suka kashe shanu da dama tare da jikkata wasu.
Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN), reshen jihar Filato, Ibrahim Babayo Yusuf, ne ya bayyana haka inda ya shaida cewa ‘yan bindigar sun kai hari yankin tare da harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sanya makiyayan suka bar shanunsu don tsira da ransu.
- Yadda Fasahar Sadarwa Ta Bunkasa A Kasar Sin Zuwa Karshen 2024
- Kirsimeti: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Shinkafa Don Tallafa Wa Kiristoci
Da yake ƙarin bayani kan faruwar lamarin a garin Jos, Ibrahim, ya bayyana cewa an kashe shanun ne a yayin da makiyayan suke kiwonsu a yankin, wanda ya ce sun kai rahoto ga jami’an tsaro na “Operation Safe Haven”, da ke yankin kana suka yi musu rakiya zuwa inda lamarin ya faru tare da shawartarsu da su kwantar da hankalinsu.
Da yake Allah wadai da harin shugaban MACBAN, ya buƙaci mambobinsa da su kwantar da hankalinsu, tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa jami’an tsaro za su binciki lamarin tare da kamo waɗanda aikata laifin, kana ya yi gargaɗi kan ɗaukar doka a hannu.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton rundunar tsaro ta “Operation Safe Haven” da ta ‘yansandan jihar Filato ba su fitar da sanarwa ga manema labarai ba game da aukuwar lamarin.