Akalla mutane 49 ne suka suka rasa rayukansu bayan wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka a kananan hukumomin Anka, Birnin Magaji a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan bindigar sun shafe tsawon kwanaki biyar suna kai hare-haren tare da yi awon gaba mutane masu tarin yawa.
- Obi Na Jam’iyyar Labour Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido
- Kwastam ta Mika Jabun Dalar Amurka Da Jirage Marasa Matuka 148 Da Ta Kwace Ga EFCC Da Sojoji
Wata majiya a garin Anka, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun fara kai hare-hare yankunansu ne tun daga farkon makon da ya gabata, kuma sun aikata aika-aikar tasu ba tare da jami’ain tsaro sun tabuka komai ba.
Mazauna kananan hukumomin Anka da Birnin Magaji sun ce a halin da ake ciki suna cikin zaman fargaba, ganin yadda maharan ke cin karensu ba babbaka.
A makon da ya gabata ne, wasu rahotanni daga babban birnin jihar, Gusau suka bayyana cewar mahara sun kutsa kai tare da sace wani manajan bankin Taj, tare da kashe wani limamin masallacin Juma’a.