Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun harbe mutum daya wanda nan take yace ga garinku nan akan titin Gana da ke unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:46 na daren Laraba.
Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar Daily trust cewa, an kashe mamacin ne a lokacin da yake kokarin kubutar da wanda masu garkuwar suka sace a wata bakar mota kirar Prado SUV.
Ya ce, an ajiye motar ne a kofar gida mai lamba 44 a titin Gana inda daya daga cikin wadanda ake zargin ya harbe mutumin, nan take yace ga garinku nan.
A cewarsa, wannan shi ne karo na biyu da ya faruwa a wannan titin Gana cikin ‘yan makonnin da suka gabata.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan reshen babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni ‘yan sandan suka fara bin diddigin masu garkuwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp