Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke Ihima, a Jihar Kogi.
A cewar wata sanarwa daga ofishin yaɗa labaran Sanatan ya fitar a Abuja ranar Alhamis, ya ce ‘yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba sun yi tunanin cewa Sanatan na garin lokacin da suka kai harin.
- Sojojin Nijeriya Sun Yi Lugudan Wuta Kan Sansanin Ƴan Ta’adda A Borno
- APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu
Sai dai jami’an Sibil Difens tare da haɗin kan mazauna yankin sun daƙile harin.
Sanata Natasha, ta bakin hadiminta Isreal Arogbonlo, ta bayyana cewa ƙaninta ya kai wasu ‘yan kwangila garinsu domin duba wuraren da za a aiwatar da wasu sabbin ayyuka da ta kawo wa yankinta.
“’Yan bindigar sun ɗauka cewa ni ce na dawo gida, sai suka kai hari gidan iyayena a daren ranar,” in ji ta.
“Na gode Allah, babu wanda ya jikkata, kuma an kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda.”
Ofishin yaɗa labaranta ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce “ƙoƙarinta na kare gaskiya da wakiltar al’ummarta bai kamata a mayar da shi barazana ko tashin hankali ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp