Da safiyar jiya ‘yan bindiga dadi suka farmaki reshen shalkwatar hukumar ‘yansanda da ke Ihiala a Jihar Anambra inda suka lalata motoci da wasu kadarori a yankin tare da tseratar da wadanda ake zargi da masu laifi ne.
Sannan kuma sun yi ta harbi kan mai-uwa da wani a sama inda suka tilasta wa mutane arcewa.
An kuma nakalto cewa ‘yan bindigan sun fasa rumbum ajiye bindigogi na ‘yansandan a yayin da suka kaddamar da harin. Sai dai babu tabbacin cewa ko sun yi awun gaba da wasu bindigi ko alburusai daga shalkwatar.
Sannan an kuma nakalto cewa ‘yansandan da ke bakin aiki a wajen sun maida martani inda suka yi musayar wuta yayin da mutanen da ke yankin suka gudu domin tsira da rayukansu.
Zuwa lokacin da wakilin LEADERSHIP ke aiko da labarin nan babu babu tabbacin ko wasu sun jikkata sakamakon harin. Sai dai ‘yan bindigan sun saki wasu daga cikin mutanen da ake zargi da laifuka daban-daban da suke tsare a caji ofishin din.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar a wannan Shalkwatar, DSP Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin sa’ilin da aka tuntube shi.
Ya ce, ‘yan bindigan sun gudu sun bar wata bindiga daya kirar AK-47 a wajen da lamarin ya faru.
Ya ce, “Da safiyar ranar 28/12/2022 jami’anmu sun fafata da wasu ‘yan bindigan da suka kawo hari reshen shalkwatar ‘yansanda da ke Iliala kuma sun kwato bindiga kirar AK-47 a wajensu. Kazalika ‘yan bindigan sun arci na kare lokacin da ‘yan sanda suka sha karbinsu sai dai babu wani da ya jikkata.”