‘Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina, inda suka kashe dakarun soji biyar tare da jikkata 11.
Sun kai harin ne da misalin karfe 2 na ranar Lahadi, harin dai ya yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama.
- Buratai Ya Goyi Bayan Shugaba Tinubu Na Hana Sojojin Kasashen Waje Kafa Sansani A Nijeriya
- An Fara Bincike Kan Yadda Jami’in Kwastam Ya Kashe Kansa A Kano
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce sama da ‘yan ta’adda 200 dauke da muggan makamai karkashin jagorancin kasurgumin dan bindiga, Ado Aleiru, suka kai hari sansanin sojoji da ke kauyen ‘Yar Malamai.
“Harin da aka kai a sansanin sojojin ya yi sanadin jikkata da kuma mutuwar jami’an sojoji,” in ji sanarwar.
Daya daga cikin ‘yan banga a yankin, mai suna Aliyu Tukur mai shekaru 30, na daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu.
“Sojoji sun kai hari su ma, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar, tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama.
Sun shafe sama da sa’o’i biyu suna bari wuta, wanda hakan ya sanya sojojin komawa zuwa wani waje mai tazarar kilomita 25, saboda kashe dakarunsu da aka yi.
‘Yan ta’addan sun same koma kauyen ‘Yar Malamai, inda suka kone gidaje da dama tare da bude wuta kan mai uwa da wabi.
Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka rayukansu ba.