A daren ranar Litinin wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a unguwar Hayin Banki da ke karamar hukumar Anka a Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu takwas.
Majiyoyi daga hedikwatar karamar hukumar sun shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 11:30 na dare inda suka yi ta harbe-harbe.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Hakimi, Sun Yi Awon Gaba Da ‘Ya’Yansa 5 A Filato
- PDP Ta Zargi Makiyan Dimokuradiyya Da Kitsa Hargitsi A Gangamin Da Jam’iyyar Ta Yi A Kaduna
Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ma’aikatan wani kamfanin ruwa da kuma manajan wata gonar kiwon kaji.
“’Yan bindigar sun shiga garin Anka ne a daren jiya, a unguwar Hayin Banki, inda suka yi garkuwa da mutane tara amma daga baya aka tsinci gawar daya daga cikin mutane taran.
Sun kuma sace dabobbi da dama, kamar yadda majiyoyin suka bayyana.
Karamar hukumar Anka dai na fuskantar hare-hare tun farkon wannan shekara kuma tana daya daga cikin kananan hukumomin da gwamnatin jihar ta rufe a baya-bayan nan.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ce rundunar ta baza jami’an tsaro a yankin kuma ana ci gaba da kokarin ganin sun dawo da zaman lafiya a yankin.
Ya ce, “Gaskiya ne, an kai gari; mun baza jami’an tsaro a yankin da nufin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba”.