An kashe mutane hudu tare da sace wasu takwas bayan wasu ‘yan bindiga da suka kai wa manoma hari a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a yankin Nahuta da Dantsuntu na karamar hukumar Batsari a jihar.
- Mutane 71 Sun Kamu Da Cutar Zazzabin Dengue A Jihar Sakkwato
- Nijar Ta Cika Shekaru 65 Da Samun ‘Yancin Kai
Wani ganau ya shaida wa Leadership Hausa cewa ‘yan bindigar sun kewaye yankin tun daga yammacin ranar Asabar a lokacin da manoman suke tsaka da aiki a gonakinsu, inda suka dinga harbe-harbe zuwa safiyar Lahadi.
Amma kakakin rundunar ‘yansandan Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ya kuma kara da cewa tuni ‘yansanda suka fara kokari domin kubutar da mutanen da aka sace.
Batsari dai na daya daga cikin kananan hukumomin Jihar Katsina da ke kan gaba inda ‘yan fashi ke karuwa.
Lamarin ya sanya mazauna yankin ke fama da wahalar shiga gonakinsu wanda ya kasance tushen rayuwarsu daya tilo.
Tashe-tashen hankula da ke da alaka da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya ya samo asali ne daga rikicin makiyaya da manoma.