Wani sabon harin da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai ya yi sanadin mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu da dama a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.Â
Daga cikin wadanda aka kashe har da shugaban kauyen Kukar Babangida, Zauren Katsina, tare da ‘ya’yansa hudu.
- Bangaren Layin Dogo Na Sin Ya Yi Jigilar Fasinjoji Mafi Yawa A 2023
- Sin Na Fatan Taimakawa Ghana Kan Matsalar Basusukan Da Ake Bin Ta
Mazauna garin sun shaida wa Leadership Hausa ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyen da sanyin safiyar Alhamis da karfe 1:30 na dare lokacin da akasarin mazauna garin ke yi barci.
An tattaro cewa kusan mutane 6,000 galibin manoma da makiyaya ne ke zaune a wannan kauye.
Kukar Babangida ya kasance daya daga cikin kauyuka masu rauni da ‘yan bindiga suka addaba a jihar.
“Ko a cikin makon, an kai hare-haren ‘yan bindiga biyu a karamar hukumar Jibia. An kaddamar da daya daga cikin hare-haren a Jibia zuwa Batsari, kuma an kai wani harin a tsakiyar garin Jibia,” in ji wani mazaunin garin.
Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina har yanzu ba ta mayar da martani kan harin ba.