Akalla mutane 26 ‘yan bindiga suka kashe hadi da sojoji bakwai a kauyen Kangon Garacci da ke karkashin gundumar Dangulbi a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin mai suna Malam Bello Dangulbi ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a Gusau.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 04:00 na yammacin ranar Litinin. ‘yan bindigar na tare da shugabansu Ali Kachalla.
Acewarsa, “‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanun da dama bayan sun yi ma wasu yankan rago, da al’umma suka fatattake su, sai suka yi wa al’ummar kwanton bauna inda suka kashe Ashirin daga cikinsu.
Bello ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kai hari kan sojoji da ke tare da jama’a. kuma sun kashe bakwai daga cikin sojojin a fafatawa da suka yi da ‘yan bindigar.
Mutane a dama sun samu raunuka wadanda a halin yanzu suke jinya a cibiyar kula da lafiya matakin farko da ke Dangulbi.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojoji ta Operation Hadarin Daji ya ci tura.