• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 6, Sun Sace 38 Tare Da Ƙone Dukiyoyi A Katsina

byEl-Zaharadeen Umar
2 years ago
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki wani kauye mai suna ‘Yan Nasarawa da ke cikin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina inda suka kashe mutane 6 sannan suka yi awan gaba da 38.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga ƙauye ne a daren ranar Litinin inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi ba kakkautawa.

  • ‘Ƴan bindiga Sun Kashe Mutum 12 A Kaduna
  • Mbappe Ya Amince Ya Koma Real Madrid Akan Kwantiragin Shekaru 5 A Karshen Kakar Wasa Ta Bana

Daga cikin waɗanda ‘yan bindiga suka kashe harda mai unguwa Malam Haruna Wakili.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto an yi jana’izar waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan hari na wuce gona da iri da ‘yan bindiga suka kaiwa wannan gari.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan kashe mutane 6 da suka yi , sun koma kone motoci 8 da shaguna 10 da gidaje 6 a cikin garin na ‘Yan Nasarawa.

LABARAI MASU NASABA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

Har ila yau wannan hari ya rutsa da shanu da dama wanda ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a san adadin su, suma tuni sun kone sakamakon cinna masu wuta da ɓarayin suka yi.

Koda muka tuntuɓi rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta bakin kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, tuni sun tura jami’an tsaro domin kewaye dajin da ɓarayin suke

Haka kuma ya bada tabbacin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa tare da gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Next Post
Murja

Zargin Baɗala: Kotu Ta Umarci A Binciki Lafiyar Ƙwaƙwalwar Murja Kunya

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version