Wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Powish da ke gundumar Kalmai, a ƙaramar hukumar Billiri na jihar Gombe, yayi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya, tare da ƙona gidaje da kwashe dabbobi da dama.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na safiyar ranar Alhamis, bayan da ‘yan bindigar ɗauke da muggan makamai da suka haɗa da adduna suka far wa ‘yan ƙauyen da dabbobinsu.
- Asibitin Gombe Ya Haramtawa Ma’aikata Yin Kiripto Lokacin Aiki
- Gwamnan Gombe Ya Aza Tubalin Gina Majalisar Dokoki Da Babbar Kotun Jiha Na Zamani
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun kuma kashe wani Yusuf Akwara, tare da ƙona gidaje yayin ƙazamin farmakin inda suka tsere kafin isowar tawagar jami’an tsaro ƙauyen wanda ke maƙwabta da jami’an tsaron kana suka tayasu kashe gobarar.
Kwamishinan Ƴansanda mai kula da jihar, CP Hayatu Usman, ya yi Allah-wadai da faruwar lamarin a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido wajen da lamarin ya faru tare da rakiyar kwamandan runduna soji na ta 301 da kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) na jihar, da kuma shugaban ƙaramar hukumar Billiri.
Ya buƙaci jama’ar da su kasance masu haƙuri tare da bai wa Ƴansanda haɗin kai wajen gudanar da bincike kan aika-aikar wanda ya ce an tura tawagar jami’ai Ƴansanda daga sashin binciken manyan laifuka na jihar don gano waɗanda suka kai harin.