Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Dabna da ke karamar hukuma Hong a Jihar Adamawa, inda suka kashe mutum uku.
Rahotannin da ke fitowa daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma kone gidaje, shagona, babura sannan suka sace wasu kayayyakin abinci.
- Dubi Ga Sabbin Hanyoyin Kutse A Facebook, WhatsApp Da Asusun Ajiyar Banki
- Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwar Duniya
Mista Samuel Naci, daya daga cikin mutanen garin ya shaida wa manema labarai cewa “Maharan sun kai harin ne a kan babura biyu, sai kawai suka fara harbe-harbe kan jama’a, inda suka kashe mutum uku” in ji Naci.
Tuni dai kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar, CP Tola Afolabi, ya yi Allah wadai da harin da ya kai ga asarar rayuka uku da dukiyoyi.
Cikin wata takardar sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Njogeroje, ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya ba da umarnin kama maharan cikin gaggawa.
“Ba za mu amince da kai hari kan mutanen da ba su ji bansu gani ba, rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar ta kare rayukan jama’a, irin wadannan miyagun dabi’u za mu tabbatar doka da hukunta masu aikata su” in ji sanarwar.