A kalla sojoji 30 da ‘yan sandan mobal 7 da kuma sauran jama’a da dama ne suka rasa rayukansu a wurin hakar ma’adanai dake karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, Sakamakon mummunan harin da ‘yan Bindiga suka kai wa Ma’aikatan a dajin.
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ta bayyana cewa, har yanzu bata tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin ba.
Sai dai kamfanin jaridar Premium times Hausa ya rahoto cewa, Mazauna yankin da lamarin ya afku sun tabbatar da cewa sune su ka fita tsintar gawarwakin bayan kura ta lafa, sun dauko gawarwakin sojoji 30 da mobal 7 da sauran gawarwaki 6 acikin dajin dake kewaye da wurin hakar ma’adanan a Safiyar ranar Alhamis.
Mazauna yankin sun ce maharan sun kwashi mutane da dama ciki har da ‘yan Chana Wadanda ke aiki da kamfanin hakar ma’adanan.
Wani shugaban matasa a Shiroro mai suna Yusuf Kokki, ya ce ana sa ran kara gano wasu gawarwakin, saboda har zuwa safiyar ranar Alhamis masu ceto na ci gaba da neman gawarwaki a cikin jejin.