‘Yan bindiga sun kai wa ‘yansanda hari a yankin ‘Yar Tsamiyar Jino da ke karamar hukumar Kankara a Jihar Katsina, inda suka kashe jami’an ‘yansanda hudu.
Daga bisani, maharan sun kone motar sintirin ‘yansandan.
- An Kaddamar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Rasha a Kazan
- An Gudanar Da Taron Tattaunawar Kafofin Watsa Labarai Na Kazan Na Kasashen BRICS
Wats majiya mai tushe ya bayyana cewa, da farko, ‘yan bindigar sun shirya kai wa matafiya da ke hanyarsu ta zuwa kasuwar Kankara daga yankin Mai Dabino hari.
Sai dai, mutanen yankin sun guje wa hanyar bayan samun labarin harin da ‘yan bindigar ke kokarin kai wa.
Bayan shirin farko ya ci tura, ‘yan bindigar sun karkatar da hankalinsu zuwa kauyen ‘Yar Tsamiyar Jino, inda wannan mummunan al’amari ya faru.
Wannan lamari ya kara tayar da hankalin jama’a game da matsalar tsaro a yankin, amma babu wata sanarwa daga rundunar ‘yansandan Jihar Katsina.