‘Yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Pankshin Kudu, Laven Denty, a gidansa da ke unguwar Dong na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A makon da ya gabata ma, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin unguwar Dong, inda suka yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), da kuma ɗalibin Jami’ar Jos.
- Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
- Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025
Masu garkuwar da mutanen sun shiga gidan iyalan Solomon Dansura, da misalin ƙarfe 10 na dare inda suka tafi da baƙinsa guda biyu a lokacin.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin jihar ko kuma tabbaci daga rundunar ‘yansandan jihar.














