Rundunar ‘yansandan Jihar Delta, ta tabbatar da sace wasu dalibai da ba a tantance adadinsu ba.
Kakkin ‘yansandan jihar, Edafe Bright ne, ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X.
- Lokaci Ya Yi Da Kasashen Yamma Za Su Yi Watsi Da Tunanin Wai Sun Fi Sauran Kasashe
- Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Tare Da Takwaransa Na Indonesia
“Rundunar ‘yansanda na sane da wannan mummunan al’amari, muna kuma daukan dukkan matakan da suka dace domin ganin an kubutar da su ba tare da sun jikkata ba.”
Rahotannin sun bayyana cewar daliban na tafiya ne cikin wata motar bas a yankin karamar hukumar Ughelli a ranar Juma’a.
Wasu majiyoyi a jihar sun bayyana cewar daliban za su iya haura 10 wadanda aka sace.
Kakakin, ya ce ba a tuntubi kowa kan neman biyan kudin fansa ba amma suna iya bakin kokarinsu don ganin an ceto su.
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Jihar Kaduna, ta tabbatar da kubutar dalibai 137 da ‘yan bindiga suka sace a garin Kuriga.
A gefe daya kuma, wasu majiyoyi sun bayyana cewar sai da gwamnati ta biya kudin fansa kafin sakin daliban.
Wannam ba shi ne karo na farko da mahara ke sace dalibai ba.
Irin hakan ta faru a jihohin Kaduna, Neja, Zamfara da Katsina, inda daliban suka shafe kwanaki kafin shakar iskar ‘yanci.