‘Yan bindiga sun sace akalla daliban makarantar Tsangaya 15 a garin Gidan Bakuso da ke Karamar Hukumar Gada a Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce an sace daliban ne daga makarantarsu da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Asabar.
- An Kammala Canja Fasalin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai
- Saudiyya Ta Shirya Karbar Bakuncin Kofin Duniya A 2034
Mai makarantar, Liman Abubakar ya shaida wa ‘yan jarida cewa dalibai 15 ne, wadanda ba a san inda suka shiga ba.
Abubakar ya ce ‘yan bindigar sun mamaye garin da misalin karfe 1 na safiyar raanr, inda suka harbe mutum guda suka yi awon gaba da wata mata.
“Yayin da suke ficewa da daga garin, sai suka hangi dalibanmu a daki a kwance, nan take suka yi awon gaba da su”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp