Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Zira da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, inda suka yi awon gaba da Hakimin Kauyen, Yahya Saleh Abubakar; da dansa Habibu Saleh.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin.
- Gwamnatin Kaduna Ta Sake Sallamar Malaman Makaranta 2,357 Daga Aiki
- Kwankwaso Ba Zai Yi Wa Peter Obi Takarar Mataimaki Ba — NNPP
Ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen da ke karkashin rundunar ‘yan sanda ta Rishi, wani kauye mai iyaka da Jihar Filato da misalin karfe 2 na daren Asabar.
Wakil ya ce kwamishinan ‘yan sanda Umar Mamman Sanda ya umurci jami’in ‘yan sanda na yankin (DPO) da ya ceto wanda aka sace ba tare da wani rauni ba.
“Tuni dai rundunar ta aike da tawagar ‘yan sanda da sauran jami’an ‘yan sanda domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma a yanzu haka jami’anmu suna daji domin neman wadanda aka sace.
“Muna tabbatar wa mazauna garin cewa nan ba da jimawa ba za a kubutar da mutanen da aka sace.”
Wakil ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum tare da kai rahoton duk wani mutum da suke zarginsa ga ‘yan sanda don yin duk mai yiwuwa don ceto wadanda lamarin ya shafa.
An yi garkuwa da mutanen ne kwanaki biyar bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Jimari da ke karamar hukumar Alkaleri, inda suka kashe mutane hudu tare da raunata uku.
Hakimin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya ce har yanzu wadanda suka yi garkuwa da mutanen ba su tuntubi danginsu ba.