A daren jiya Alhamis da misalin Karfe 1 na wayewar garin Juma’a, wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun shiga Garin Kahutu da ke yankin Ƙaramar hukumar ÆŠanja a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Hajiya Halima Adamu, mahaifiya ga shahararren mawakin nan Dauda Adamu Kahutu Rarara.
Rahotannin da muka samu daga Æ™auyen sun nuna cewa, maharan sun shiga kauyen ne a Æ™afa a sirrince ba tare da yin harbi ba a lokacin da suke gudanar da ta’annacin nasu.
Sun dauki ‘yan mintuna suna farmaki kuma gyatumar ba ta yi musu gardama ba lokacin da suka bukaci ta bi su kamar yadda muka samu labari.
An bayyana cewa akwai sauran mutane a cikin gidan, amma maharan suka zabi ɗaukar mahaifiyar Rarara, inda suka bar sauran kuma ba wanda ya yi ƙoƙarin martani ga maharan.
Ana zaton maharan sun ajiye ababen hawansu a wani wuri inda suka taka da ƙafa wajen shiga ƙauyen.
Jin ta bakin shahararren mawaƙin ya ci tura kasancewar baya ɗaga wayarsa a idan an kira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp