‘Yan bindiga sun kai hari garin Na-Alma da ke yankin karamar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina , inda suka kone gidaje, sannan suka yi awon gaba da mata, har da masu juna biyu, da kananan yara, da wani wanda ‘yan bindiga suka taba sare wa hannu da kafa tare da kashe wani mai unguwa.
Bayanai sun ce, hare-haren ‘yan bindigan na baya-bayan nan sun jefa mutane da dama cikin tsaka mai wuya.
- Mun Damu Da Matsalar Yara ‘Yan Shila A Adamawa – Fintiri
- Ka Sallami Duk Wanda Ya Gaza Kokari A Gwamnatinka – El-Rufai Ga Tinubu
Wata majiya a yankin ya ce: “Tun wajen 8:30 na dare muka shaida wa jami’an tsaro amma ba su zo ba har sai da mutanen nan suka shiga suka fara harbi, sai dai kawai su ce ga su nan zuwa, amma ba su zo ba.
“Hakan ya sa har sai da suka gama kone-kone da duk abin da za su yi sannan suka zo.
“Asarar da muka yi Allah ne kadai Ya san yawanta saboda haka suka bi gida-gida suka kone kuma duk manyan gidaje ne suka kone sun kuma kashe mai unguwa.”
Majiyar ta ce ba ta san adadin mutanen da suka sace ba, amma tana kyautata zaton sun kai 20.
“Idan aka hada da matan da yaran da wannan Alhajin za su kai mutum 20.”
Mutanen yankin sun ce suna fuskantar hare-haren ‘yan bindiga fiye da kowane lokaci.
Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu ya danganta wannan harin a matsayin na ramuwar gayya.
Ya ce harin na zuwa ne sakamakon halaka wani mutum da ake zargin kasurgumin dan bindiga ne da mukarrabansa, wadanda suka addabi yankin karamar hukumar Malumfashi da kewayenta.