‘Yan bindiga sun tare babbar hanyar Gusau-Funtua a safiyar ranar Alhamis, inda suka sace matafiya.Â
Wani da maharan suka tsare mai suna Yusuf Tsafe, ya shaida cewa ‘yan bindigar sun tare titin da misalin karfe 7 na safe, a yankin Tazame.
- Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan $1.5 Sakamakon Yin Bahaya A Fili
- Kasar Sin Na Goyon Bayan Warware Sabanin Dake Tsakanin Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ta Hanyar Tattaunawa
‘Yan bindigar, sun zo yankin a kan babura kimanin 50, kuma kowane yana dauke da mutane uku, inda suka yi awon gaba da matafiya da ba a san adadinsu ba.
Tsafe, ya ce suna tsaye a gefen hanya suna jiran sojoji su bude hanya, yayin da suka ga ‘yan bindigar suna kwashe mutane zuwa cikin daji.
Sojojin sun isa wajen kuma an jiyo suna harbe-harbe, amma an dauki tsawon sa’o’i ba a bude hanyar ba.
Wani matafiyi ya tabbatar da cewa hanyar Magazu zuwa Kucheri, wadda ta hada Gusau da Funtua, ita ma ‘yan bindiga sun tare ta.
Dukkanin matafiyan sun ce sojoji sun umarce su da su tsaya har sai an bude hanya.
Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta tabbatar da cewa an tura karin jami’ai, ciki har da ‘yansandan kwantar da tarzoma, zuwa yankin.
Jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa Maso Yamma na fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.