Wasu da ake kyautata zaton cewa ‘yan bindiga ne, sun yi garkuwa da wani magidanci a kan titin Sabon Lugbe da ke hanyar zuwa titin jirgin saman Abuja.
Lamarin ya faru ne a lokacin da mutumin da matarsa ke kan hanyar komawa gida, inda wasu da ke cikin mota kirar Golf suka bude musu wuta.
- AFCON 2023:Tanzania Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Maroko
- An Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Lalata Da ‘Yar Shekara 15
Hakan ya sanya suka tsaya ba shiri saboda fasa tayoyin motar da ‘yan bindigar suka yi.
Wata makociyar wadanda lamarin ya faru da su, Daramola Joseph, ta bayyana wa manema labarai cewa bayan motar ta tsaya ne matar mutumin ta gudu, inda shi kuma mijin suka tafi da shi.
Sai dai kakakin rundunar ‘yansandan Abuja, SP Adeh Josephine, ta ce za ta bincika abin da ya faru dangane da wannan harin.
Wannan harin dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 da ‘yan bindiga suka shiga wani rukunin gidajen sojoji da ke Kurudu a Abuja, inda suka yi awon gaba da mutane da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp