• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 1, Sun Harbe Wasu 2 A Kano

by Sadiq
3 years ago
Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum mai shekaru 60 a duniya tare da harbe wasu biyu a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rano a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Manman Dauda, ​​ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Kano a ranar Talata.

  • An Haramta Wa Limamai Karanta Alkur’ani Daga Waya A lokutan Sallolin Dare A Kuwait
  • Gwamnatin Bauchi Ta Ja Kunnen Masu Wa’azi Kan Amfani Da Kalaman Tunzura Jama’a

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 1:30 na dare.

Ya ce ‘yan sandan sun samu labarin ne da misalin karfe 01:30 na dare cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rano, inda suka yi awon gaba da wani Alhaji Na’ayya Gangarbi.

Dauda ya ce, nan take rundunar hadin gwiwa ta jami’an sintiri na sashen JTF da kuma masu yaki da masu garkuwa da mutane suka garzaya wurin.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa an kwashe wasu mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga – Maskuru Ukaisha a kafarsa ta dama da Salisu Ibrahim a kafadarsa ta hagu, inda aka garzaya da su babban asibitin Rogo domin samun kulawa.

A cewarsa, an tura karin jami’an tsaro dauke da makamai zuwa yankin domin bibiyar ’yan bindigar da duk wasu bata-gari da ke kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin.

“Jami’an tsaro dauke da makamai da sauran tawagar dabara tare da ‘yan banga an tura yankin domin samun nasarar ceto wadanda abin ya shafa,” in ji shi.

Ya ce an fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suka sace tare da kubutar da wadanda abin ya shafa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
Manyan Labarai

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara
Manyan Labarai

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025
Next Post
El-Rufai Ya Jinjina Wa Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Danwasa A Kaduna

El-Rufai Ya Jinjina Wa Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Danwasa A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.