Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Sarki Obalohun na Okoloke a karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi, Oba James Dada Ogunyanda a fadarsa.
Garkuwa da Oba Ogunyanda da sanyin safiyar Alhamis ya jefa jihar cikin firgici, musamman karamar hukumar Yagba, inda aka ce sace-sacen mutane ya zama ruwan dare.
- ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed
- Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, wasu gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki fadar sarkin da ke garin Okoloke ne da misalin karfe 2 na tsakar dare.
An ce, ‘yan bindigar sun yi galaba a kan masu gadin fadar, inda suka tafi da sarkin zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ‘yansandan jihar Kogi ta ce, an fara gudanar da bincike, inda ta ce rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an tsaro da ‘yan banga na yankin sun fara farautar ganowa tare da kubutar da sarkin.
Sai dai shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Hon. Tosin Olokun ya yi Allah-wadai da sace Sarkin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp