’Yan bindiga sun sako wani ɗan kasuwa mazaunin Katsina, Anas Ahmadu, tare da matarsa mai juna biyu, Halimatu, da kuma ’yarsu ’yar shekara biyu bayan shafe kwanaki 21 a hannunsu.
Wani daga cikin dangin ma’auratan ne ya tabbatar da sakinsu a ranar Alhamis, inda ya ce an biya kuɗin fansa Naira miliyan 50 kafin ’yan bindigar su sako su.
- Yadda Jama’a Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis
- Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
“Alhamdulillah! ‘yan bindiga sun sako Anas, Halimatu da ’yarsu. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta dawowa gida, amma sai da aka biya Naira miliyan 50,” in ji ɗan uwan.
An sace ma’auratan ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025, a gidansu da ke Filin Canada Quarters, Katsina.
Da farko, ’yan bindigar sun buƙaci Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa, amma daga baya suka rage kuɗin zuwa Naira miliyan 50 kafin su sako su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp