Wasu ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba sun sace mahaifiyar dan takarar kujerar Sanatan Jigawa ta tsakiya, Tijjani Ibrahim Gaya.
Mahaifiyar tasa mai shekaru 70 a duniya, Hajiya Jaja dai an yi garkuwa da ita ne a gidanta da ke karamar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa.
- Sanatocin APC 3 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP da NNPP
- Dan Takarar Gwamnan Katsina A NNPP Ya Ba Da Tallafin Miliyan 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shisu, ya ce lamarin ya faru a ranar Talata, inda ya ce masu garkuwan sun mamayi gidanta inda suka tafi da ita da karfi duk da girman shekarunta.
Ya ce, bayan samun rahoton faruwar lamarin, nan take kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarnin tura jami’ai na musamman da kokarin ceto ta.
DSP Shisu ya kara da cewa, da hadin guiwar sojojin da ‘yan sanda za su tabbatar da cafko masu hannu a lamarin tare da gurfanar da su, ya roki jama’a da su ke taimaka musu da bayanai masu aikata laifuka.
Wata majiya daga karamar hukumar Kiyawa ta shaida wa LEADERSHIP cewa masu garkuwan da yawansu ya Kai 15 zuwa 20 ne cikin motoci uku suka kutsa kai tare da tursasa wa dattijowar gami da saceta zuwa wani wajen da ba a sani ba.
Wannan lamarin na zuwa ne kasa da makonni uku da sace mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, daga bisani aka ceto ta.