Wasu da ake zargin cewa, ‘yan Bindiga ne sun sace malaman Coci biyu a jihar Kaduna.
Malaman sune, Rabaran John Cheitnum da Rabaran Donatus Cleopas, an sace su ne a yankin Yadin Gura da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
A cikin sanarwar da Shugaban Cocin Catholic Diocese, Rabaran Emmanuel Okolo ya fitar ya ce, Rabaran Cheitnum shi ne shugaban kungiyar CAN ta kasa reshen karamar hukumar Jama’a da ke jihar Kaduna.
Talla
Ya ci gaba da cewa, an sace su ne a ranar juma’a 16 ga watan Yuli, a Cocin Catholic da ke a yankin Yadin Gura.
Talla