Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Dogon Daji da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, inda suka kashe hakimin garin ta hanyar yi masa yankan rago.
Shugaban ƙaramar hukumar, Garba Shehu Tsafe, ya tabbatar da faruwar lamarin a daren ranar Litinin.
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
- Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
Ya ce a ranar ɗin ma ‘yan bindigar sun sake tare hanyoyi da ke kai wa Gusau.
Shugaban ya danganta ƙaruwa irin wannan hare-hare da sulhun da ake yi a jih6ar Katsina, yana mai cewa hakan yana bai wa ‘yan bindigar damar kai farmaki a wasu wurare.
Masana tsaro kuma sun daɗe suna gargaɗi cewa yin sulhu da ‘yan bindiga ba zai kawo mafita ba, domin sau da yawa suna amfani da shi ne wajen samun mafaka bayan sun kai hari.