‘Yan bindigar da suka sace tsohon mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado, sun bukaci a biya su Naira miliyan 70 kudin fansa.
Wata majiya ta shaida wa Leadership Hausa a Lafiya, babban birnin jihar cewa, ‘yan bindigar sun tuntubi iyalansa.
- Gwamnatin Kaduna Ta Dage Dokar Hana Fita A Chikun
- Firaministan Malaysia: Shawarar Wayewar Kan Kasa Da Kasa Za Ta Taimaka Wajen Tinkatar Matsaloli
A baya wakilinmu ya ruwaito cewa an yi garkuwa da Onje Gye-Wado da safiyar ranwr Juma’a a kauyen Gwagi da ke karamar hukumar Wamba.
Majiyar ta kara da cewa ’yan uwansa sun roki wadanda suka sace shi da su karbi Naira miliyan biyu maimakon Naira miliyan 70 da suka nema saboda rashin samun kudi da ake fama da shi.
Ya ce, “Tuni wadanda suka yi garkuwa da shi suka tuntubi iyalan Farfesa kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan 70, amma mun roke su da su karbi Naira miliyan biyu saboda ba za mu iya tara abin da ya wuce haka ba sakamakon hutun da Gwamnatin Tarayya ayyana na esta.”