Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya koka da sake bullar kungiyar Boko Haram a jihar, yana mai cewa sabbin hare-haren na nuni da cewa gwamnati na kara samun nakasu a shirin samar da zaman lafiya.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin wani taro na musamman kan tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati, wanda ya samu halartar babban hafsan runduna ta 7, Manjo Janar Abubakar Haruna, da kwamandojin sashe, da kwamishinan ‘yansanda, da sauran shugabannin hukumomin tsaro, da sarakunan gargajiya.
- Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
- Trump Ya Dakatar da Harajin Da Sanya Wa Ƙasashen Duniya, Ya Ƙi Cire Wa China
Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa da yanayin tsaron da jihar ke ciki a halin yanzu, yayin da ya jaddada cewa ana samun sabbin hare-haren Boko Haram da sace-sacen jama’a a al’ummomi da dama, kusan a kullum ba tare da wani tarnaki ba, ya nuna cewa Jihar Borno na kara samun koma-baya. Musamman ganin a halin yanzu kungiyar tana mamaye da wasu sassan jihar.
Ya ce, “A yayin da nake jawabi a wannan muhimmin taro a yau, abin takaici ne yadda ake ci gaba samun sabbin hare-haren Boko Haram da sace-sacen jama’a a al’ummomi da dama, kusan kullum ba tare da wata arangama da jami’an tsaro ba, ya nuna cewa hakan ba karamin koma-baya ne ga Jihar Borno ba.
Zulum ya koka da cewa hare-haren da aka kai kwanan nan da ya yi sanadiyyar tarwatsa sansanonin sojoji a Wajirko, Sabon Gari a Karamar Hukumar Damboa, Wulgo a Gamboru Ngala, Izge a Karamar Hukumar Gwoza, da sauran kashe-kashen da aka yi wa fararen hula da jami’an tsaro, da cewa abu ne da yake bukatar a nuna damuwa matuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp